Kungiyar malaman jami’oin Najeriya ta dakatar da yajin aiki

Kungiyar malaman jami’oin Najeriya ta dakatar da yajin aikin watanni uku da ta shafe ta na yi. Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan cimma yarjejeniya da ta ce ta yi da gwamnatin tarayya a yammacin jiya Alhamis kan bukatunta. Shugaban kungiyar ASUU Farfessa Biodun Ogunyemi ne ya bayyanawa manema labarai hakan, kuma ya ce […]

Kungiyar malaman jami’oin Najeriya ta dakatar da yajin aiki

Wani zaman sulhu da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar ASUU

Kungiyar malaman jami’oin Najeriya ta dakatar da yajin aikin watanni uku da ta shafe ta na yi.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan cimma yarjejeniya da ta ce ta yi da gwamnatin tarayya a yammacin jiya Alhamis kan bukatunta.

Shugaban kungiyar ASUU Farfessa Biodun Ogunyemi ne ya bayyanawa manema labarai hakan, kuma ya ce kungiyar ta gabatarwa gwamnatin tarayya bukatunsu da gwamnati ta rattabawa hannu tun a shekarar 2013.

Kungiyar ASUU ta bukaci jami’o’in kasar da yau Juma’a 8 ga Fabirairu 2019 su dawo bakin aikinsu don ci gaba da gudanar da harkokin jami’o’in.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta