Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya sun dakatar da yajin aiki

Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya da Kere-Kere (ASUP) ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta kwashe wata biyu tana gudanarwa. Kungiyar ta sanar da wannan mataki da ta dauka ne a ranar Talata da ta gabata. Shugaban Kungiyar ASUP, Malam Usman Dutse ne ya sanar da dakatar da yajin aikin a yayin da yake […]

Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya sun dakatar da yajin aiki
Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya sun dakatar da yajin aiki

Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya da Kere-Kere (ASUP) ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta kwashe wata biyu tana gudanarwa. Kungiyar ta sanar da wannan mataki da ta dauka ne a ranar Talata da ta gabata.

Shugaban Kungiyar ASUP, Malam Usman Dutse ne ya sanar da dakatar da yajin aikin a yayin da yake ganawa da ’yan jarida a Abuja.

Malam Usman ya ce a yayin da suke yajin aikin, sun gudanar da tarurruka daban-daban a tsakaninsu da wakilan gwamnati dangane da abin da ya shafi dabbaka yarjejeniyar da aka yi da su a shekarar 2017, bayan da suka kawo karshen yajin aikin da suka gudanar a waccan shekarar.

Ya ce sun kawo karshen yajin aikin ne bayan sun jima suna tuntubar kungiyoyin kwadago takwarorinsu da ke kasar nan. “Mun janye yajin aikin nan bisa sharadin cewa gwamnati za ta waiwayi alkawarin da aka yi na dabbaka kudirorin da aka cimma a 2017. Matukar kuma ba a dabbaka wadannan kudirori ba, to kungiyarmu za ta zartar da matakin da ta ga ya fi dacewa a gaba,” inji shi.

Wadansu daga cikin al’amuran da suke cikin bukatun nasu, kamar yadda ya ce sun hada da yanke musu wani adadi na kudaden albashi, maganar karin girma da aka dade ba a yi musu ba da kuma kudaden alawus-alawus da ba a biyansu da sauran bukatu daban-daban da suke na ka’ida.