kungiyar Mamaye ta bukaci a ware kasafi mai tsoka ga fannin lafiya
Shugaban Cibiyar Tabbatar da Adalci (Centre for Social Justice) Barista Eze Onyekpere ya bukaci a rika ware kaso mai yawa kan harkokin kiwon lafiya a kasafin kudin kasar nan tare da tabbatar ana aiki da kasafin.Barista Eze Onyekpere ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron tattaunawa da kungiyar […]
Shugaban Cibiyar Tabbatar da Adalci (Centre for Social Justice) Barista Eze Onyekpere ya bukaci a rika ware kaso mai yawa kan harkokin kiwon lafiya a kasafin kudin kasar nan tare da tabbatar ana aiki da kasafin.
Barista Eze Onyekpere ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron tattaunawa da kungiyar MamaYe/Ebidence for Action, wata kungiya da ke kokarin ganin an ware wa fannin lafiya kaso mai tsoka a kasafin kudi tare da tabbatar ana aiki da kasafin yadda ya kamata, ta shirya wa manema labarai a Abuja a ranar Talatar da ta gabata.
Barista Eze Onyekpere ya kuma ce bai kamata Shugaban kasa ya je kasar waje jinya ba, bayan kudin da aka ware wa asibitin Fadar Shugaban kasa a kasafin bana ya fi kudin da aka ware wa manyan asibitocin koyarwa 10, inda ya ce, kuma bai kamata a rika magana a kan kashi nawa za a ba kowane fanni ba, domin idan aka duba kashin da wani fanni yake bukata za a samu ya kai sama da kashi 100.
Ya ce ya kamata ne a fara magana a kan yaya aka yi da kudin da aka kebe wa fannin kiwon lafiya domin a tabbatar an yi amfani da su yadda ya kamata.
Barista Eze ya kara da cewa ya kamata mahukunta a fannin kiwon lafiya su zama masu yin abu a fili, sannnan ya bukaci ’yan jarida su taimaka wajen ganin cewa an aiwatar da abin da aka ware kudi dominsa a fannin lafiya, kuma su tabbatar cewa sun sa ido sosai kan yadda ake kashe kudaden.
A jawabin Shugaban kungiyar Kula da Lafiyar Iyali kuma Shgaban Kwamitin Bayar da Sahawara na kungiyar Tsarin Iyali da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu ta Najeriya, Farfesa Oladapo Ladipo ya ce ya kamata a rika lura sosai wajen magance matsalar mace-macen mata yayin haihuwa, inda ya ce bai kamata a ce mata suna yawan mutuwa lokacin haihuwa ba.
Farfesa Oladapo ya kara da cewa, ya kamata mutane su lura da shirin tazarar haihuwa domin yana taimakawa wurin rage mutuwa yayin haihuwa.
Game da zuwan Shugaban kasa zuwa kasar waje domin duba kunnensa, ya ce ba wai babu masana a harkar kunne ba ne a Najeriya, sai dai rashin kayan aiki na zamani da rashin bincike da ake fama da shi a Najeriya.
Ya ce ya kamata gwamnati ta kara zuba kudi a harkar kiwon lafiya domin a samu kayan aiki na zamani wanda hakan zai sa likitocin Najeriya su nuna kwarewarsu a wurin aiki.
An tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kiwon lafiya da gudanar da kasafin kudi kan kiwon lafiya da rawar da manema labarai za su taka wajen tabbatar da ana aiwatar da tsare-tsaren kiwon lafiya da aiwatar da kasafin kiwon lafiya yadda ya kamata.