kungiyar Manazarta Harsuna ta karrama Dokta Bukar Usman
A yau Juma’a ne aka kammala Taron kungiyar Nazarin Harsunan kasashen Yammacin Afrika, “West African Languages Congress” (WALC) da babban taro na 26 na kungiyar Masu Nazari Kan Harsunan Najeriya, mai taken “Conference Of The Linguistic Association Of Nigeria” (CLAN), wanda suka yi bikin cika shekaru 50 da kafuwa.A yayin taron na kwanaki 3 da […]
A yau Juma’a ne aka kammala Taron kungiyar Nazarin Harsunan kasashen Yammacin Afrika, “West African Languages Congress” (WALC) da babban taro na 26 na kungiyar Masu Nazari Kan Harsunan Najeriya, mai taken “Conference Of The Linguistic Association Of Nigeria” (CLAN), wanda suka yi bikin cika shekaru 50 da kafuwa.
A yayin taron na kwanaki 3 da aka gudanar a Jami’ar Ibadan, an karrama Dokta Bukar Usman, saboda irin gudunmawar da ya dade yana bayarwa ta fannin rubuta littattafan tatsunuyoyi a cikin harsunan Hausa da Turanci, wadanda suke taimakawa a fafutukar bunkasa harsuna a Najeriya da duniya baki daya.
Masana a kan harsuna da suka hada da Farfesa Beban Sammy Chumbow na Jami’ar Yaounde a kasar Kamaru da manyan malamai na ciki da wajen Najeriya ne suka gabatar da kasidu daban-daban a wajen taron na bana, mai taken ‘Bincike Da Tabbatar Da Ajiyar Littattafai Da dorewar Bunkasar Harsuna A kasashen Yammacin Afrika.’
Sakataren kungiyar Masu Nazari Kan Harsuna Najeriya kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), Farfesa Andrew Haruna, tare da tallafin Mataimakin Shugaban Jami’ar Ibadan (UI), Farfesa Ayo Bamgbose, su ne suka mika wa Dokta Bukar Usman, takardar satifiket da sauran kyutuka na shaidar wannan karramawa da kungiyar ta CLAN ta yi masa, wanda ta ce ya cancanta ta yi masa wannan karramawa.
daruruwan mahalarta taron, maza da mata sun yi ta taba hannaye da kalmomin jinjinawa ga Dokta Bukar Usman, domin taya shi murnar samun wannan muhimmiyar kyautar girmamawa.
Wakilinmu ya samu tattaunawa da Dokta Bukar Usman, mai shekaru 70 da haihuwa, wanda ya ce yanzu haka yana zaman kansa ne bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati a Ofishin Shugaban kasa, a 1999.
“Tun daga wancan lokaci na ci gaba da rubuce-rubuce ne har zuwa yanzu da wadannan kungiyoyi masu nazarin harsunan Najeriya da kasashen Afrika suka yi nazarin irin rubuce-rubucen da na yi, suka ga ya cancanta su ba ni wannan kyutar karramawa. Na yi rubuce-rubuce ne a kan al’amuran da suka shafi gwamnati da tarihin ni kaina. Daga baya kuma, sai na mayar da hankali ta fannin rubuce-rubucen littattafan tatsunuyoyi, wanda yanzu haka akwai littattafan tatsunuyoyi da harshen Hausa guda 15 da guda 4 na Turanci da ake amfani da su a kasashen duniya.” Inji Dokta Bukar.
Da wakilinmu ya tambaye shi ko mene ne dalilin da ya sa ya mayar da hankali ga rubutun tatsunuyoyi da harshen Hausa, alhali shi ba Bahaushe ba ne? Sai ya amsa da cewa: “A gaskiya ni ba Bahaushe ba ne, na fito ne daga kabilar Babur ko Bura a yankin Biu, cikin Jihar Borno kuma na lura cewa kabilarmu ba su da yawa idan aka kwatanta ta da yawan Hausawa, domin yawan kabilarmu bai wuce rabin miliyan ba. Idan kuwa kana so ka isar da irin wannan sakon hannunka mai sanda da koyarwa tare da wayar da kan al’umma, dole ne ka yi amfani da harshen kabila mafi yawn jama’a a cikin al’umma. Saboda sha’awar da nake yi wa harshen Hausa, wanda kafofin yada labarai na kasashen duniya da suka ci gaba suke amfani da shi wajen isar da sako ga al’umma, shi ne dalilin da ya sa na fï mayar da hankali wajen yin rubuce-rubucen nawa a cikin harshen Hausa, domin ina so harshen ya kara bunkasa da ci gaba a duniya.”
Marubucin ya ci gaba da cewa: “Ba zan manta da irin littattafan da na karanta a lokacin muna makarantar firamare ba, kamar “Ka Koyi Karatu” da “Ka Yi Ta Karatu” da “Magana Jari Ce” wadanda marigayi Abubakar Imam ya rubuta, wadanda akwai muhimman darussa da na koya daga cikinsu da ba zan manta da su ba. Amma a lokacin da na fara karanta na Turanci, sai na lura cewa yawancin labaransu duka tatsuniyoyi ne wanda na fahimci cewa, idan Turawa sun yi nasu da Turanci, to me zai hana mu ma mu nemi abubuwan da za mu rubuta a cikin harsunan da mutanenmu, musamman yara kanana za su rika karantawa; domin amfanin rayuwarsu wanda a yanzu haka babu irin wadannan littattafai na tatsunuyoyi sun bace? Da yawa daga cikin yaran namu har da wadanda suka je jami’a, idan ka tambaye su labarin tatsunuyoyi sai ka ji sun ce ba su sani ba, wanda haka babbar illa ce da ke haifar da tabarbarewar ilmi.”
Haka kuma marubucin ya bayyana yadda ya fara rubuta littattafan nasa, inda ya ce: “A lokacin da na buga littattafan nawa, na ga yadda mutane suka karbe su da muhimmanci sosai, wanda abin bai tsaya a nan gida kadai ba, har ya isa zuwa kasashen waje wanda a yau din nan ina matukar farin cikin cewa, a Jami’ar Cairo, kasar Masar, ana yin amfani da littattafan nawa wajen yin digiri na daya da na biyu da na uku. Tun daga lokacin da na fara rubuce rubucen tatsunuyoyi, bayan na bar aikin gwamnati, ni ban san cewa mutane suna karanta su ba. Wallahi, ni ban san mutanen da suka bayar da sunana ga kungiyar da ta girmama ni da lambar yabo ba, sai dai kawai Shugabar kungiyar ta CLAN, ta aiko mani da wasikar cewa suna so su karrama ni a wannan taro nasu na Ibadan, ga shi kuma ya tabbata. Ka ga ikon Allah ke nan, ni dai sai godiya, Alhamdu lillahi. Domin ban taba tunanin cewa irin abubuwan da na rubuta har sun isa a karrama ni da su ba. Ni dai na yi ne saboda in samu littattafan da yara za su rika karantawa a nan gaba kamar yadda mu ma aka tanadar mana a lokacin muna kananan yara. Yanzu haka muna kokarin ganin an mayar da wadannan littattafan tatsuniyoyi zuwa cikin majigi, sai dai mun lura cewa, mutanenmu ba su da ilmin fahimtar haka a Najeriya.”
Da yake amsa wata tambaya, Dakta Bukar ya ce, shi dai sai godiya ga Allah domin ba wani babban marubuci ba ne amma ga sunansa ya shiga kundin tarihin duniya. “Yau da kullum ce ta sa aka karrama ni a kan rubutu kuma mai kishin harshen Hausa. Ina kishin harshen Babur da na fito daga cikinsa, wanda saboda ganin cewa wasu harsuna sun fara bacewa daga doron kasa shi ne yasa na fara shirin buga wani littafi a kan yadda wasu harsuna a Najeriya da wasu kasashe suke bacewa. Na lura cewa, akwai harsuna 207 a kasar Austireliya kafin Turawa su ci kasar da yaki amma a yau din nan saura harsuna 7 kadai ake amfani da su a wannan kasa. Haka mu ma a Najeriya a sashen Bauchi, akwai harsuna kamar guda 7 da suka bace. Kamar yadda aka yi bayanai cikin kasidu a wajen wannan taro na kungiyar ta CLAN, an nuna cewa idan ba ka yin amfanin rubutu da karatu da harshe to kuwa hanyar mutuwar wannan harshe kenan.”
Dakta Bukar Usman, wanda ya kafa Gidauniyar tallafa wa mutane mai suna “Dr. Bukar Usman Foundation,” ya yi karin bayani dangane da irin rayuwar da yake ciki a yanzu, ya ce: “Ban dogara da rayuwata a kan littattafan da na buga ba, domin ni ba na sayar da wadannan littattafai, yawancinsu ina bayar da su kyauta ne ga mutane da makarantu da gidajen rediyo da talabijin da dakunan laburare. Na dogara da kudin fansho da nake karba da kuma aikin da na yi wa kaina tanadi bayan na bar aiki. Yanzu haka akwai littattafai guda 4 da na fara aikin rubuta su. Na daya ina yi ne a kan tarihin kasar Biu, wato mahaifata, wanda na yi nisa a kan wannan littafi. Sai na biyu da nake rubutawa a game da yadda ’yan matan kasar Biu suka soma karatun zamani. Akwai littafi na uku a kan batun bacewar harsuna da kuma littafin tatsunuyoyi, wadanda nake kyautata zaton za a kammala su a cikin shekara mai zuwa.”
Da yake magana dangane da tanadin masu gadon wannan rubuce-rubuce a cikin ’ya’yansa ko kabilarsa, sai ya ce: “Bayan rasuwata sai a bar komai ga Allah. Idan ’ya’ya ko kabilata sun yi sha’awar gadon irin wannan rubuce-rubuce, ya rage gare su amma ni dai na fi so a bar komai ga Allah. A lokacin da mutum yake da karfinsa sai ya yi abin da zai iya yi.”