kungiyar Manoman Rani ta yi kira ga gwamnatin Barno
A kokarin da suke yi na inganta harkar noma a Jihar Borno, kungiyar Manoman Rani ta bukaci gwamnatin jihar ta bunkasa hanyoyin inganta noman irin na zamani ta yadda matasa za su ci moriyar sana’ar.Shugaban kungiyar, Alhaji Kyari Gambo ne ya fadi hakan a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Maidugri. “Mu manoman ranin […]
A kokarin da suke yi na inganta harkar noma a Jihar Borno, kungiyar Manoman Rani ta bukaci gwamnatin jihar ta bunkasa hanyoyin inganta noman irin na zamani ta yadda matasa za su ci moriyar sana’ar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Kyari Gambo ne ya fadi hakan a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Maidugri. “Mu manoman ranin jihar, musamman na bangaren Tafkin Chadi, wanda ya hade yankunan kananan hukumomin Marte da Ngala da Kala Balge da kuma yankin karamar Hukumar Abadam, muna noma hektoci sama da dubu dari 6, wato kwatankwacin daruruwan buhunan hatsi da sauran kayayyakin abinci irin su shinkafa da alkama da kuma albasa da sauransu. Sai dai muna fuskantar wasu matsaloli na yadda idan gwamnati ba ta shigo ciki ta tallafa mana ba, sha’anin man zai durkushe. Matsalolin sun hada da rashin taraktocin Noma da isowar takin zamani a kan lokaci da isassun kudaden gudanarwa. Sannan muna bukatar gwamnati ta turo mana malaman gona don duba ayyukanmu tare da ba mu shawarwari kan dabarun zamani wajen bunkasa harkar. Idan aka yi haka, za a samar da isasshen abinci da kuma aikin yi ga matasa don magance zaman kashe wando”.
Shugaba Kyari ya kuma shawarci ’yan uwansa manoman su ci gaba da hakuri da juriya kan rungumar wannan sana’a tasu hannu bibbiyu, lamarin da zai sa su cimma burinsu. Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni su rika sayen kayan noman don kara musu karfin gwiwa.
A nata bangaren, gwamnatin Jihar Borno ta ce burinta ne ta habaka harkar noma a jihar, kamar yadda kwamishinan aikin gona, Alhaji Usman Zanna ya fada a wani taron manema labarai da ya kira kwanan baya. “Gwamnati ta raba taraktoci kan rahusa, tare da kokarin samar da takin zamanin a kan lokaci, sannan ta dauki nauyin matasa 50 ya zuwa kasar Thailand don koyo dabarun noman zamani da niyyar su koya wa manoman jihar”. Inji shi.