kungiyar Marayu da Zawarawa ta raba kekunan dinki a Kafanchan

kungiyar Marayu da Zawarawa ta raba kekunan dinki guda takwas da takardar shaidar kammala koyon dinki ga wadansu marayu da zawarawa bayan daukar nauyin koyar da su sana’ar dinki a garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a a ke Jihar Kaduna. A lokacin da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Sakataren kungiyar, Malam Salihu dankaka, […]

kungiyar Marayu da Zawarawa ta raba kekunan dinki a Kafanchan

kungiyar Marayu da Zawarawa ta raba kekunan dinki guda takwas da takardar shaidar kammala koyon dinki ga wadansu marayu da zawarawa bayan daukar nauyin koyar da su sana’ar dinki a garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a a ke Jihar Kaduna.

A lokacin da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Sakataren kungiyar, Malam Salihu dankaka, ya ce an kafa kungiyar ce shekaru fiye da goma da suka wuce inda a da sukan raba kayan taimakon abinci ne kawai ga marayu amma zuwa yanzu sun hada da daukar nauyin koyar da su sana’ar dinki tare da ba da kekunan dinki kyauta ga wadanda suka jure kuma suka ci jarrabawar kammala samun horo.

Malam dankaka, ya ce zuwa yanzu kungiyar ta yi nasarar daukar nauyin karatun yara 95 daga firamare zuwa sakandare, sannan ta bangaren kiwon lafiya sukan biya wa yaro daga Naira dubu biyu zuwa kasa, kuma suna aiwatar da haka ne ta hanyar harajin da suke sanya wa kansu sai kuma gudunmawar da Masarautar Jama’a da sauran jama’a ke taimaka musu da ita.

Malaman da suka gabatar da jawabin jan hankali a taron sun yi kira ga mahalarta su rika tallafa wa marayu da zawarawa domin zuba jari ne don Ranar Sakamako.

Sheikh Aminu kassim, Shugaban kungiyar Fityanul Islam na Kudancin Kaduna ya ce duk wanda ya tallafa wa ’ya’yan wadansu, Allah Zai kawo wanda zai taimaka wa nasa ko bayan ba ya duniya inda ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin su mayar da hankali ga abin da suka koya su kuma amfanar da wadansu.

Shi kuwa Malam Musa Imam, Babban Na’ibin Limamin Jama’atu Izalatil Bidi’ah na karamar Hukumar Jama’a kira ya yi ga daliban da aka yaye su rike amanar da aka damka musu domin Allah zai tambaye su. Sannan ya yi kira ga jama’a su gaggauta yin katin zabe da katin zama dan kasa saboda tsare mutuncin kansu.

Yayin da yake gabatar da jawabinsa, Uban kungiyar Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad, nuna godiyarsa ya yi ga Allah da kuma jagororin kungiyar bisa jajircewarsu wajen daukar wannan nauyi da kuma kokarin saukewa sannan ya nanata yin kira kan mallakar katin zabe ga jama’arsa.

Yayin da yake amsa tambayar wakilin Aminiya bayan kammala taron, Shugaban kungiyar, Alhaji Muhammad Umar, ya ce kungiyarsu na lalubo ’ya’yan da iyayensu suka rasu da zawarawan da ba su da galihu ne daga kowace kusurwa na garin Kafanchan domin ba su horo inda sukan yi haka ne ta hanyar tuntubar mambobin kungiyar don nemo irin wadannan mabukata. A karshe ya nuna farin cikinsa da irin wannan rana tare da fatan ganin na gaba lafiya.