kungiyar marubuta littattafan Hausa ta zabi sabbin shugabanninta

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Inuwar Marubuta Littattafan Hausa (Hausa Authors Forum) ta gudanar da zaben sabbin shugabanninta. Tun da farko, ‘yan kwamitin riko na kungiyar karkashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge (anka) sun bayyana makasudin kafa su, wato cewa an kafa su ne da niyyar su shirya taro kuma su gabatar kamar […]

kungiyar marubuta littattafan Hausa ta zabi sabbin shugabanninta
kungiyar marubuta littattafan Hausa ta zabi sabbin shugabanninta

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Inuwar Marubuta Littattafan Hausa (Hausa Authors Forum) ta gudanar da zaben sabbin shugabanninta.

Tun da farko, ‘yan kwamitin riko na kungiyar karkashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge (anka) sun bayyana makasudin kafa su, wato cewa an kafa su ne da niyyar su shirya taro kuma su gabatar kamar yadda ya wakana .A cewar Sakataren Kwamitin Rikon, Almujtaba Habibullahi “Kamar yadda aka sani an kafa kwamitin namu na riko domin mu shirya zabe tare da
gabatar da wannan taron kamar yadda yake wakana a yanzu” In ji shi sai dai Sakataren ya bayyana cewa kwamitin nasu bai gaji komai daga tsofaffin shugabannin kungiyar ba.
Bayan jawabin shugabannin riko, sai aka gabatar da shugabannin zabe, inda su kuma suka tantance ‘yan takara. Daga bisani kuma membobin kungiya suka fara gudanar da zabe bisa tsarin kundin tsarin mulki na kungiyar. Sabbin shugabannin da suka sami nasarar lashe zaben sun hada da Habibu Hud Ahmad Darazo a matsayin Shugaba, sai Umma Sulaiman ‘Yan’awaki inda ta zama Mataimakiyar Shugaba. Haka kuma akwai Kabir Yusuf Fagge (anka) a matsayin Sakatare. Sai Lawan Muhammad PRP a matsayin Mataimakin Sakatare. Shi kuwa Jamilu Haruna Jibeka shi ya zama Sakataren Kudi ,sai Hafsat Ahmad Zabiyar Faira a matsayin Ma’aji. Zahraddeen Nasir kuwa shi ne Jami’in hulda da jama’a na daya ,sai Fauziyya D. Sulaiman a matsayin jami’ar hulda da jama’a ta biyu. Abubakar Auyo shi ne Jami’in Walwala. Sai Almujtaba Habibullah wanda shi ya zama Jami’in Saye da Sayarwa, Almustafa A. Muhammad shi ne Mai bincike na daya, yayin da Adamu Yusuf Indabo ya kasance Mai bincike na biyu. A jawabinsa na kammala zaben, Shugaban Zaben, Malam Kabiru Shu’aibu(Hannu daya) ya mika godiya ga ‘ya’yan kungiya da suka ba da hadin kai har aka gudanar da zaben lafiya aka tashi lafiya. Shi ma a nasa jawabin sabon Shugaban kungiyar Habib Hud Darazo ya yi godiya ga ’yan’uwansa ‘yan kungiyar bisa zabarsa da suka yi, sannan ya yi alkawarin tafiyar da al’amuran shugabancin kungiyar bisa amana.

Barau ya buƙaci Ganduje ya ƙwato wa APC ƙarin jihohi

An kama masu laifi 30,000 a 2024 – Sufeto Janar na ’Yan Sanda

DAGA LARABA: Dalilan wasu darikun Kirista ba sa bikin Kirsimeti

PCAACC ta karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano