kungiyar Marubuta Ta Najeriya za ta farfado da harkar rubutun Hausa
kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) za ta sake duba yiyuwar gyara da fasalin tsarin rubuce-rubece a Arewa don bai wa harshen Hausa muhimmanci da bunkasa marubutan Hausa a Najeriya da ma duniya baki daya. Hakan zai sake mayar da daraja da kwarjinin marubutan Hausa a cikin al’umma.Babban Jami’in Hulda Da Jama’a na kungiyar (Arewa), Malam […]
kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) za ta sake duba yiyuwar gyara da fasalin tsarin rubuce-rubece a Arewa don bai wa harshen Hausa muhimmanci da bunkasa marubutan Hausa a Najeriya da ma duniya baki daya. Hakan zai sake mayar da daraja da kwarjinin marubutan Hausa a cikin al’umma.
Babban Jami’in Hulda Da Jama’a na kungiyar (Arewa), Malam Yusuf Dingyadi ne ya bayyana haka lokacin da yake hira da ’yan jarida a ofishinsa da ke Jihar Sakkwato.
Jami’in ya bayyana cewa ya zama dole a sake fasalin tsarin rubuce-rubucen kasar nan don dacewa da marubutan Hausa wadanda suke da muhimmanci ga ci gaban harshen Hausa da al’adun Hausawa, ta yadda za a kara wa matasa karfin gwiwar fahimtar harshen Hausa da kuma karatun Hausa a makarantu da kuma sauran wuraren hulda da jama’a.
“Ba shakka sabuwar tafiyar kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), za ta mayar da hankali ga fito da sababbin dubaru na bunkasa daraja da kwarjinin malam Bahaushe tare da gyara da kuma inganta hanyoyin Hausawa da al’adunsu.” Inji Yusuf Dingyadi
Ya kuma nuna bukatar da ke akwai na hada kai tsakanin manyan ’yan siyasa, masu hannu da shuni, sarakunan gargajiyya da kuma sauran malaman addini wajen bunkasa harshen Hausa da kuma maido da darajar karatunsa.
Ya kara da cewa, akwai damuwa ganin yadda mafi rinjayen matasa da kuma al’ummar yankin Arewa suka yi watsi da al’adun Hausa, suka dauko na aro daga waje don gudanar da rayuwarsu, sakamakon rashin isasshen bayani dangane da wannan harshen mai daraja.
Da yake bayani game da sababbin shugabannin kungiyar da aka zaba a taron kasa-da-kasa na 34 na kungiyar da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar ta makon jiya, ya ce Alhaji Denja Abudullahi ne ya lashe zaben zama sabon shugaban kungiyar; yayin da Camillus Ukah ya zama Mataimakin Shugaba da Ofonime Inyang ya samu zama Sakatare Janar. Sai Hajiya Hasiya Muhammad da ta zama Ma’aji.
Fiye da marubuta 450 daga ko’ina cikin Najeriya da wasu daga kasashen Ghana, Nijar, Kamaru, Ingila da Canada suka halarci taron na kwanaki uku a garin Kaduna.