Kungiyar Masoya buhari ta yi gargadi ga masu yin amfani da qabilanci
Kungiyar Masoya buhari Zalla (kMbZ) ta ja kunnen kungiyoyin da ke kokarin yin amfani da kabilanci don raba kan kasar nan. Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Garba Haruna shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon da ya gabata. Haruna ya bayyana cewa kungiyoyin na yin amfani […]
Kungiyar Masoya buhari Zalla (kMbZ) ta ja kunnen kungiyoyin da ke kokarin yin amfani da kabilanci don raba kan kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Garba Haruna shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon da ya gabata.
Haruna ya bayyana cewa kungiyoyin na yin amfani da kabilanci ne don cimma burinsu na siyasa.
“Wadannan kungiyoyi da suka kunno kai suna wasu maganganu da ba su dace ba na kabilanci suna nuna cewa akwai baraka tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa suna yi ne don cimma bukatar kansu kawai amma ba don kawo gyara ko cigaban kasa ba,” inji shi.
Ya bayyana cewa duk wata magana da wani zai kawo wacce ke nuna akwai baraka tsakanin shugaban kasa da mataikinsa karya ne.
Ya zargi wasu daga cikin manyan ’yan siyasar kasar nan da daurewa kungiyoyin gindi don cimma burinsu na siyasa.
Ya dage a kan cewa burin irin wadannan ’yan siyasa bata-gari ba zai cika ba da yardar Ubangiji.
don kamar yadda ya ce shugaban kasa da mataimakinsa kansu a hade yake kuma tuni suka zama tsintsiya madaurinki daya.
Saboda haka sai ya ja hankulan ’yan Najeriya su yi kunnen-uwar-shegu da duk wani dan siyasa da yake yada jita-jita.
Ya yaba wa Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo dangane da kokarin da yake yi na rike gaskiya da amana.
daga nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa shugaba buhari addu’ar samun lafiya tare da fatan ganin ya dawo ya ci gaba da mulki.
Ya dage a kan cewa samun lafiyar buhari babu shakka ita ce alheri ga kasar nan musamman idan aka yi la’akari da nasarar da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa da karya lagon kungiyar boko Haram.
Ya bayyana cewa kungiyarsu tuni ta kammala shirye-shiryen tarbar shugaba buhari idan ya dawo daga kasar birtaniya.