kungiyar masoya Manzon Allah sun yi bikin mauludi na musamman

kungiyar  masoya Manzon Allah da ’yan gidansa da ke Jihar Legas ta gudanar da biki na musamman don tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah tare da wa’azi daga manyan malamai daban-daban.Bikin mauludin, wanda aka fara shi tun daga karfe bakwai na daren Asabar har zuwa wayewar garin Lahadi, ya gudana ne a unguwar Daji da […]

kungiyar masoya Manzon Allah sun yi bikin mauludi na musamman

kungiyar  masoya Manzon Allah da ’yan gidansa da ke Jihar Legas ta gudanar da biki na musamman don tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah tare da wa’azi daga manyan malamai daban-daban.
Bikin mauludin, wanda aka fara shi tun daga karfe bakwai na daren Asabar har zuwa wayewar garin Lahadi, ya gudana ne a unguwar Daji da ke yankin Agege.
Mataimakin shugaban kungiyar na farko, Malam Muhammad Jamilu Sani Mairago ya bayyyana cewa sun gudanar da mauludin ne don tunatar da jama’a kyawawan dabi’un Manzon Allah. “Mu kullum muna tuna Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba wai sai cikin watan da aka haife shi ba kawai. Saboda haka mun shirya mauludin ne don nuna kauna da soyayya gare shi kuma burinmu shi ne mu samu tsarkake aiki, Allah da ManzonSa su yarda da mu. Shi ya sa muka gayyaci malamai daban-daban don su gudanar da wa’azi daga ciki da wajen Najeriya”.
Bako na musamman a wurin taron, Shaik Muhammed Kabiru Yusuf ya bayyana farin cikinsa dangane da gayyatar da aka yi masa, inda ya ce dole musulmi su gode wa Allah saboda kyautar da Ya yi musu ta Manzon Allah. “Kyautar da Allah Ya yi mana ta ManzonSa, ta cancanci mu gode maSa, to shi ya sa muke yin wannan mauludi don nuna soyayyarmu da kaunarmu ga Annabi. A dunkule ina so na ja hankalin musulmi da cewa mu rike Manzon Allah, kada mu bari wani abu ya rude mu. Kuma mu rike abubuwan da Manzon Allah ya koya mana da son addini da kaunar junanmu. Saboda haka kada mu kuskura mu saki Manzon Allah”.
daliban makarantar Islamiyya ta Al-Madrasatul Islamiyyatul Islamiyya da ke unguwar Daji a yankin Agege ta gudanar da karatun Diwani a wurin mauludin, karkashin jagorancin malamin makarantar Malam Abdurrahman Gambo, wanda ya ce sun karanta diwani ne domin nuna soyayya ga Manzon Allah tare da cusa so da kaunar Annabi a zukatan daliban makarantar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban karamar Hukumar Agege da wakilan gwamnatin Jihar Legas da sarakunan Hausawa na jihar da malamai daga jihohin Kaduna da Kano da kuma manyan malamai daga kasar Ghana da Murteniya da sauran kasashe daban-daban

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50