kungiyar masu cin naman matattun mutane a kasar Indiya tana bunkasa

Wata kungiyar jama’a masu cin naman matattun mutane kuma suna gadajen kwanciya a kawunansu, sai kara bunkasa take, musamman saboda yadda jama’a ke tururuwar shiga cikinta, kamar yadda kafar yada labarai ta Mirror ta fitar.Mutanen, wadanda ake kira da sunan Aghori, suna zaune ne gefen rafin Ganges da ke Arewacin kasar Indiya, kuma sukan bursune […]

kungiyar masu cin naman matattun mutane a kasar Indiya tana bunkasa

Wata kungiyar jama’a masu cin naman matattun mutane kuma suna gadajen kwanciya a kawunansu, sai kara bunkasa take, musamman saboda yadda jama’a ke tururuwar shiga cikinta, kamar yadda kafar yada labarai ta Mirror ta fitar.
Mutanen, wadanda ake kira da sunan Aghori, suna zaune ne gefen rafin Ganges da ke Arewacin kasar Indiya, kuma sukan bursune jikinsu da tokar matattun mutane da akan kona. Haka nan suna shan duk abin shansu a cikin kokon kan mutane.
Duk da naman matattun mutane suke ci, amma jama’ar karkara da ke yankin suna tsoron su.
Wani mai sana’ar daukar hoto dan kasar Ireland mai suna Darragh Mason, mai shekara 37, ya sami damar zama na dan wani lokaci cikin irin wadannan mutane, wadanda ya ce yawansu karuwa yake duk da irin dabi’ar rayuwarsu.
Darragh ya ce, “An san su da tsamo matattun mutane daga cikin rafin na Ganges suna ci.  Sukan tattara kokunan kawunan mutane da sauran kasusuwan jiki da inda akan kona gawawwaki, suna amfani da su wajen gudanar da wadansu tsafe-tsafensu.  Suna da imanin cewa wai iko yakan fito ne daga matattu.
“Akwai lokacin da suka yi kokarin jan hankalina don in sha ruwan rafin Ganges da aka zuba a cikin kokon kan mutum, amma kimanin mita biyu daga gefen gabar rafin, wadansu kuma suna kona gawarwaki, sai na kasa sha.  Na yi amannar cewa lallai akwai rubudin cututtuka a cikin rafin”.
Darragh ya ci gaba da cewa, da yawa hankalin wasu jama’a kan jawu zuwa ga wadanda dabi’a. Misali, akwai wani Ba’amerike da ya zauna da su na tsawon wani lokaci.  “Wadannan mutane sukan yi duk dabi’ar da za ta nuna su kaskantattu ne a tsakanin jama’a, saboda haka ma ba safai sukan sanya suturar kirki ba.  Hasali ma sau da yawa gashin kansu yakan kasance hargitsai, ba tsari”. Inji shi.
Duk da irin halin da suke ciki, wadannan mutanen na Aghori, suna da halin bayar da taimako ga jama’a, musamman suka gina wata farfajiya ta kutare, inda aka kula da masu ciwon kuturta  99,045 da kuma wadanda ke da alamunta su147,503.