Kungiyar Masu Cutar Laka ta nemi gwamnati ta tallafa mata

kungiyar Masu fama da cutar laka a Jihar Kano ta nemi gwamnatin jihar da ta samar da wani yanayi da za ta rika tallafa musu wajen daukar nauyin yi musu aiki, don sawwaka musu tsadar jinyar da suke fama da ita. Shugaban kungiyar Injiniya Abdul D. Haruna ne ya yi wannan kiran yayin da kungiyar […]

Kungiyar Masu Cutar Laka ta nemi gwamnati ta tallafa mata

kungiyar Masu fama da cutar laka a Jihar Kano ta nemi gwamnatin jihar da ta samar da wani yanayi da za ta rika tallafa musu wajen daukar nauyin yi musu aiki, don sawwaka musu tsadar jinyar da suke fama da ita.

Shugaban kungiyar Injiniya Abdul D. Haruna ne ya yi wannan kiran yayin da kungiyar ta kai ziyara ga ofishin Jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Kano.

Injiniya Abdul ya bayyana cewa kasancewar cutar laka cuta ce wacce ke cin kudi wajen kula da masu ita akwai bukatar gwamnati ta shigo ciki don ganin an ceto masu cutar daga shiga wani hali “duba da cewa wanann cuta tana bukatar kashe kudi wajen yin aikin IMR wanda ake gudanarwa.

Lokaci-lokaci ya sanya wasu daga cikinmu ba su da halin da za su rika samun kulawar da suke bukata saboda yanayin rayuwa. Akwai mai wanann lalura da ya kasance a yanzu haka ba shi da komai duk wani abu da ya mallaka ya kare hatta katifar da yake kwanciya sai da ya sayar da ita don neman magani, don haka muke ganin zai yi kyau idan gwamnati ta shigo cikin lamarinmu ta tallafa mana. Kun ga a yanzu idan za a yi wa mara lafiya IMR a kowane bangare na wuraren jinyarsa to ana yi akan kudi Naira dubu sittin zuwa saba’in.”

Har ila yau Shugaban kungiyar ya yi kira ga gwamnati da ta samar da wani bangare guda da za a rika kula da masu irin wannan cuta a sabon asibitin Giginyu, domin a rage cinkoso a asibitin kashi na Dala “A yanzu asibitin kashi na kasa da ke Dala ya cika babu wurin da za a kula da masu jinya, don haka muke kira ga gwamnati da ta ware wani daki guda a sabon asibitin da ta samar na Giginyu wanda har aka samar da injin IMR a ciki wato injin a ake amfani da shi wajen yi wa masu lalura irin tamu aiki, domin kula da masu lalurarmu. Idan aka yi haka cinkoson da ake Asibitin kashi zai ragu kwarai da gaske kuma masu lalurarmu za su samu kulawar da suke bukata”

Da yake nuna damuwarsa game da halin da masu lalurar ke ciki, shugaban kungiyar ya bayyana cewa ta kai a yanzu mutanensu sai dai su tafi garin Jos don samun tallafin kujerun da suke amfani da su wajen zama wato wheelchairs “kasancewar wasu daga cikin masu lalurarmu ba su da halin samun kujerun zama, sukan tafi har Jos don neman tallafin wadannan kujerun domin a can akwai kungiyoyin da ke bayar da irin wanann taimako. Kun ga da a nan jihar za a samu wasu kungiyoyin ko daidaikun mawadatanmu a ce suna taimaka mana to da lamarin zai zo da Sauki.”

Ya ce manufar da ta sa suka kafa kungiyar ta su shi ne domin wayar da kan mutane game da yadda wannan cuta take domin jama’a su fahimci irin lalurar da kuma bukatar masu wannan lalura “Yawancinmu ba mu san cutar ba sai da ta same mu, don haka muka ga akwai bukatar jama’a su san wani abu game da wannan cuta da kuma irin bukatun da masu lalurar ke nema. Muna ganin sanin hakan zai yi amfani fiye da a ce sai lokacin da mutum ya sami lalurra zai san ta.

Ya kuma bayyana cewa duk da halin lalurar da suka sami kansu  bai sa sun kashe zuciyarsu sun zama  mabarata a tituna ba “ kun gan mu anan ba mu bari cutar nan ta kassara mu mun zama mabarata ba, a cikinmu akwai ma’aikata, akwai ‘yan makaranta wadanda suna zuwa jami’a suna daukar karatu. Da yawa a cikinmu suna cikin halin wannan lalura suka koma karatu suka yi digiri har da digiri na biyu. Haka kuma a cikinmu wasu sun yi aure suna kuma haihuwa kamar sauran jama’a masu lafiya. Ta bangaren mata ma lalurar ba ta hana su aure har da haihuwa. Ya danganta da irin yanayin ciwon da mutum ya sami kansa a ciki. Muna so jam’a su fahimci haka. Abin da kawai ake bukata shi ne mutum ya yarda da cutar da kuma mai ita”

Ya kuma kata da cewa baya ga aikin wayar da kan al’umma game da cutar, kungiyar tasu na kokarin wayar da kai tare da karfafa gwiwar sabbin mutanen da suka sami wannan lalura don su fuskanci yadda za su bullowa cutar da yadda za su rika kula da kansu ta hanyar nuna musu cewa ba wai samun lalurar yana nufin karshen rayuwar mutum ba “muna kokarin ba masu lalaurar kwarin gwiwa cewa su dauke mu a misali domin ga mu mun dauki shekeru masu yawa a cikinta kuma muna ci gaba da rayuwa cikin farin ciki tare da gudanar da sauran mu’amaloli na rayuwa. Sannn muna ba su kwarin gwiwa game da yadda za su fuskanci rayuwa nan gaba.

Wannan bangare kuwa bai bar mata a baya ba, muna da mata da ke wannan aikin wayar wa ‘yan uwansu kai game da cutar da yadda za su dauki kansu cikin al’umma”