Kungiyar Masu Faci ta Kasa ta yi barazanar tafiya yajin aiki
Kungiyar Masu Facin Taya ta Kasa ta ce idan gwamnatoci a dukan matakai suka ci gaba da nuna halin ko-in-kula da harkokin kungiyar, za su tafi yajin aiki nan ba da dadewa ba. Shugaban Kungiyar a shiyyar Arewacin kasar nan Kwamared Abdulrahaman Yakubu ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Lafiya, […]
Kungiyar Masu Facin Taya ta Kasa ta ce idan gwamnatoci a dukan matakai suka ci gaba da nuna halin ko-in-kula da harkokin kungiyar, za su tafi yajin aiki nan ba da dadewa ba.
Shugaban Kungiyar a shiyyar Arewacin kasar nan Kwamared Abdulrahaman Yakubu ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Lafiya, Jihar Nasarawa.
Ya ce masu facin taya a kasar nan baki daya suna ba da gagarumin gudummawa a bangaren ayyukansu amma abin takaici gwamnatoci a duka matakai ba sa tallafa musu wajen inganta harkokinsu.
Shugaban ya ce mambobin kungiyar a kasa baki daya suna fuskantar matsaloli a harkokinsu na faci da suka hada da rashin kayan aiki da rashin wurin aiki da rashin kudi ko da rance ne daga wajen gwamnati don ba su damar bunkasa ayyukansu. Ya ce sau da yawa idan aka yi sa’a gwamnati ta ba su gudunmawar kayan aiki ko wani tallafi makamancin haka, maimakon a kawo musu kai-tsaye sai a rika bi ta hannun ’yan siyasa wadanda a cewarsa ba su da alaka da kungiyar, inda a karshe sai su rika sayar wa mambobinsu da tsada.
Ya kara da cewa idan kungiyar ta tafi yajin aiki ba shakka hakan zai shafi kowa musamman shugabannin kasar nan, kasancewa kusan kowa a kasar nan yana da abin hawa ko yana yin amfani da abin hawa da ke amfani da taya.
Daga karshe sai ya yaba wa Shugaban Kungiyar a Jihar Nasarawa dangane da ayyuka da yake yi musamman na hadin kan mambobin kungiyar waje guda, inda ya bukace shi ya dore a haka. Daga nan sai ya yi kira ga mambobinsu a shiyyar Arewa da kasar nan baki daya su rika bai wa shugabanninsu cikakken goyon baya musamman wajen halartar tarurrukan kungiyarsu kuma rika ba da tasu gudunmawa a yayin tararrukan don ci gaban kungiyar baki daya.