kungiyar masu fataucin busasshen kifi ta nemi agajin gwamnatoci

kungiyar masu fataucin busasshen kifi da kwadi daga Arewa zuwa birnin Ibadan, a Jihar Oyo sun nemi agajin gwamnatoci kan halin da suke shiga wajen gudanar da harkokinsu.Alhaji Bellon Jega, wanda shi ne mataimakin shugaban kasuwar ‘yan kifi ta Arisekola da ke Bodija, a Ibadan, a hirarsu da wakilinmu ya bayyana cewa duk ranakun Alhamis […]

kungiyar masu fataucin busasshen kifi ta nemi agajin gwamnatoci

kwandon busassun kwadikungiyar masu fataucin busasshen kifi da kwadi daga Arewa zuwa birnin Ibadan, a Jihar Oyo sun nemi agajin gwamnatoci kan halin da suke shiga wajen gudanar da harkokinsu.
Alhaji Bellon Jega, wanda shi ne mataimakin shugaban kasuwar ‘yan kifi ta Arisekola da ke Bodija, a Ibadan, a hirarsu da wakilinmu ya bayyana cewa duk ranakun Alhamis da Juma’a da Asabar da Lahadi sai manyan motocin tirela dauke da nau’ukan busasshen kifi har da kwadi, daga jihohin Borno da Kebbi, sukan sauke lodi a kasuwar.
Ya ce suna hulda da masu bukatar kayan daga sassa daban-daban na jihohin Yamma, kuma kowace tirela tana dauke da kayan fiye da Naira miliyan 7. “Mun shekara fiye da 20 muna gudanar da wannan sana’a, amma ba mu taba samun tallafin gwamnati ba. Mun dade da kafa kungiyar gama kai da muke neman tallafi daga karamar Hukumar Ibadan ta Arewa ko kuma ta mika bukatarmu ga gwamnatin jiha, amma shiru kake ji. Shi ne dalilin da ya sa muka tuntubi wannan jarida Aminiya, ta taimaka wajen isar da bukatarmu ga Gwamna Abiola Ajimobi, wanda shi da kansa yake yin yekuwa ga ‘yan kasuwa su kafa kungiyoyi domin samun irin wannan tallafi”. Inji shi.
Ya ce matsala ta biyu da suke fuskanta ta shafi gwamnatocin jihohin Arewa da motocinmu suke ratsowa kafin isowa Ibadan, inda ake samun wasu jami’ai har da ‘yan banga da suke tsare motocin suna tilasta su biyan wasu haramtattun kudaden haraji, wanda tirela daya tana biyan fiye da Naira dubu dari.
“Muna ganin gwamnatocin suna sane da komai, amma sun yi gum da baki, lamarin da dole ya ja rika samun karin hauhawar farashin kifi. Muna fata gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi za su dauki matakan shawo kan wannan babbar matsala”. Inji shi.
Ya ce wannan harka tasu tana taimaka wa gwamnati da jama’a baki daya ta fuskar samun kudin shiga da ayyukan yi, musamman lokacin kakar kifi, inda hada-hadar take bunkasa. “Ka ga mun samar da guraben ayyuka ga dimbin mutane, sannan kuma mun taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin kasa, saboda haka mu ma ya kamata a taimaka mana wajen bunkasa namu harkokin”.
A karshe ya roki mahukunta a Jihar Oyo su taimaka wajen tsawata wa masu takura wa kananan ‘yan kasuwa da ke shiga unguwanni suna tallar kifin a Kwando, wadanda a wasu lokuta ake yi musu wasoson kayansu.
Ya ce a bangarensu suna jan kunnen mutanensu kan yanke wa kansu hukunci, maimakon haka, sai su kai kukansu ga shugabanninsu domin a warware kowane lamari, ta yadda za a sami zama lafiya da kwanciyar hankali.