kungiyar masu fiton kaya ta gudanar da zanga-zanga a Legas
kungiyar masu fiton kaya na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke yankin Ikeja a jihar Legas sun gudanar da zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu kan kudin da kamfanonin jiragen saman kasashen ketare ke karba daga gares u.daruruwan ‘yan kungiyar ne suka shiga zanga-zangar wadanda suka taru a bakin sakatariyar kungiyar da ke harabar filin […]
kungiyar masu fiton kaya na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke yankin Ikeja a jihar Legas sun gudanar da zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu kan kudin da kamfanonin jiragen saman kasashen ketare ke karba daga gares u.
daruruwan ‘yan kungiyar ne suka shiga zanga-zangar wadanda suka taru a bakin sakatariyar kungiyar da ke harabar filin jirgin saman, a makon da ya gabata. Daga bisani sun karasa sashen da ake sauke kaya don bayyana kokensu.
daya daga cikin masu zanga-zangar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya ce kudin da kamfanonin jiragen saman suke karba daga wurinsu ya saba wa doka. Ya ce: “Babu inda za ka samu wannan a duniya sai kasar nan. Saboda idan aka turo mana kaya daga kasashen waje an riga an biya kamfanonin tun daga can dalili da haka bai kamata a ce suka kara karbar wani kudi daga wurinmu ba don kawai za su ba mu takardun shaida,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “ban da kudin da muke biya na ka’ida ga hukumar kwastam da sauran hukumomi. Kamfanonin jiragen saman kasashen ketare na karbar daga abun da ya kama Naira 30 zuwa 35 a kowane kaya da ya kai nauyin kilo daya. Saboda haka muna so su daina cajin mu kudin da ba ya kan ka’ida.”
Masu zanga-zangar sun rika daga kwalaye dauke da rubutu kamar: “Kamfanonin jiragen saman kasashen waje, ku daina karbar kudin da ba ya kan ka’ida” da “Kamfanonin jiragen saman kasashen waje ku daina tatsar ’yan Najeriya” da “Mun yi Alla-wadai da duk wani kudi da ya saba wa doka” da sauransu.
Masu zanga-zangar sun nufi ofishin Hukumar Kwastam suna wake-wake da raye-raye. Daga bisani ’yan sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba masu hayaki mai sa hawaye.