Kungiyar masu Keke NAPEP ta bukaci Gwamnan Filato ya tallafawa matasa
Shugaban Kungiyar Masu Keke NAPEP reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, Malam Dahiru Hassan ya yi kira ga Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya tallafa wa kungiyar, ta hanyar sayo Keke NAPEP don a raba wa ’ya’yan kungiyar bashi, kamar yadda ake yi a wasu jihohin kasar nan. Malam Dahiru Hassan ya […]
Shugaban Kungiyar Masu Keke NAPEP reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, Malam Dahiru Hassan ya yi kira ga Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya tallafa wa kungiyar, ta hanyar sayo Keke NAPEP don a raba wa ’ya’yan kungiyar bashi, kamar yadda ake yi a wasu jihohin kasar nan.
Malam Dahiru Hassan ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos, inda ya ce, ban da Keke NAPEP 500 da gwamnatin Filato da ta gabata ta saya ta raba wa matasa bashi, tun zuwa wannan gwamnati ba ta sake sayen Keke NAPEP ta rabawa matasa ba.
Ya ce, don haka muna rokon gwamnatin Filato a karkashin Gwamna Simon Lalong ta sayi Keke NAPEP ta raba wa matasa bashi, kamar yadda wasu jihohi suka yi a kasar nan.
A cewar Dahiru akwai gwamnonin jihohi da suka sayi Keke NAPEP, suka raba wa matasansu, don su samu abin yin sana’a.
Dahiru Hassan ya ce, gwamnatin Lalong ta yi alkawarin za ta samar wa matasa aikin yi, kuma ta fara cika wannan alkawari da ta yi. Amma akwai bukatar ta tallafa wa masu Keke NAPEP, domin ita ma wata sana’a ce da take samar wa dubban matasa ayyukan yi.
Har ila yau ya yi kira ga gwamnatin Filato ta kammala aikin gyara hanyoyin cikin garin Jos da suka lalace, domin lalacewar da hanyoyin suka yi, na ci wa ’ya’yan kungiyar da sauran al’ummar birnin tuwo a kwarya.
Kuma ya yi kira ga gwamnatin ta gyara Babbar Kasuwar Jos saboda muhimmancin kasuwar ga jihar da Najeriya baki daya.
Ya ce, idan aka gyara kasuwar dubban matasa za su samu abin yi na kasuwanci da sana’o’i.
Daga nan ya yi godiya ga ’ya’yan kungiyar kan yadda suka tsaya wajen ganin an gudanar da zabubbukan da suka gabata cikin kwanciyar hankali da lafiya tare da bin doka da oda.