kungiyar masu maganin gargajiya za ta gina asibiti a Katsina
kungiyar masu maganin gargajiya ta kasa (National Association of Nigeria Traditional Medicine Practitional -NANTMP), reshen Jihar Katsina, ta sha alwashin gina asibitin gargajiya ta farko a jihar. Mataimakiyar shugaban kungiyar ta kasa, mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Umma ‘Yarbaiwa ta shaida haka a wani taron fadakarwa tare da wayar da kai a kan […]
kungiyar masu maganin gargajiya ta kasa (National Association of Nigeria Traditional Medicine Practitional -NANTMP), reshen Jihar Katsina, ta sha alwashin gina asibitin gargajiya ta farko a jihar.
Mataimakiyar shugaban kungiyar ta kasa, mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Umma ‘Yarbaiwa ta shaida haka a wani taron fadakarwa tare da wayar da kai a kan manufofi da kudurori da ayyukan kungiyar ga membobinta, a dakin taro na ma’aikatar jin dadi da walwala da ke kofar Durbi, a karshen makon jiya a Katsina.
Taron, wanda aka shirya wa masu amfani da na’urar amsa-kuwwa da masu shimfida, mai taken ‘Gari ya waye’, ya samu halartar membobin kungiyar da ke kananan hukumomi 34 na jihar.
Hajiya Umma ta ce kungiyar ta samu gudunmawa daga wasu kananan hukumomi kamar babura 4 da kekuna 10 tare da kudin mai daga karamar Hukumar Bindawa da ke yankin Daura; sai kuma karamar Hukumar kafur a yankin Funtuwa, wadda ta ba su wurin jinyar mahaukata, wanda suke gyarawa da ingantawa.
Ta ce a yanzu kungiyar ta dukufa a wajen ganin an samu akalla mutum 3 daga kowace karamar hukuma da za su samu takardar amincewa daga hukamar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) da kuma canza fasalin mazubi ko ajiyar magunguna don tafiya da zamani. “A yanzu haka muna kokarin bude asibitin gargajiya a nan jihar ta Katsina, wadda za ta zamo ta farko a shiyyar”. Inji ta.
A karshe sai ta ja hankalin masu maganin da su rika sa tsoron Allah duk lokacin da za su bayar da magani. Ta ce, “Mun yi nisa da shirye-shirye a tsakaninmu da jihohin Zindar da Maradi da Tawa da ke kasar Nijar don magance bata-garin masu magani a tsakaninmu. Mun yi zama uku da su a kan wannan hadin gwiwa”.
Shi kuwa shugaban masu amfani da amsa-kuwwa (lasifika) na kasa, Alhaji Bello Funtuwa tunasar da masu amfani da amsa-kuwwar ya yi a kan dokar kungiyar na bude kayansu daga karfe 6 na safe tare da rufewa a lokutan sallah, sannan kuma su tashi karfe 10 na dare.
A nasu sashen, jami’an tsaro na kungiyar, karkashin Malam Ilyasu Zakiru, sun ce ba za su daga wa duk wanda ya karya dokar kungiyar kafa ba, kuma za su tabbatar an tsare dokokin don tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da masu hulda da su.
karshe kungiyar ta yi kira ga gwamnan jihar ya kara ba ta duk taimakon da ya kamata don bunkasa harkokin kiwon lafiya a jihar ta fuskar maganin gargajiya, kamar yadda kasar Sin (China) take a yanzu ta wannan fuska.