Kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu sun koka kan haraji
Kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu ta Kasa (NAPPS) reshen Jihar Kano ta koka kan yadda gwamnati ke tatsarsu da sunan biyan haraji lamarin da ke neman jefa ’ya’yan kungiyar a halin ni-’ya-su. Shugabar Kungiyar Hajiya Maryam Magaji ce ta yi wannan koke yayin da take tatatunawa da manema labarai a bikin ranar masu makarantu […]
Kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu ta Kasa (NAPPS) reshen Jihar Kano ta koka kan yadda gwamnati ke tatsarsu da sunan biyan haraji lamarin da ke neman jefa ’ya’yan kungiyar a halin ni-’ya-su.
Shugabar Kungiyar Hajiya Maryam Magaji ce ta yi wannan koke yayin da take tatatunawa da manema labarai a bikin ranar masu makarantu masu zaman kansu da aka gudanar a Kano a makon jiya.
Hajiya Maryam Magaji ta ce abin yana damunsu yadda gwamnati ke sanya su biyan haraji barkatai, “Muna fuskantar matsalar maimaicin biyan haraji. Za ka sa mu mutum ya biya harajinsa sai kuma a sake dawowa a nemi ya biya wani harajin ta wata sigar. Wannan abin damuwa ne lura da cewa an kara dora mana biyan harajin da ka riga ka biya. Kamata ya yi a tsaya a fitar da haraji na hakika wanda mutum zai biya. Idan gwamnatin jiha ce ko karamar hukuma za ta karba to a tsaya a bar wa wanda zai karba a tsakaninsu,” inji ta.
Hajiya Maryam ta koka game da yadda gwamnatin ba ta bibiyar ayyukan da suke gudanarwa a makarantunsu, kuma gwamnatin ba ta shirya ba su horon sanin makamar aiki ba, “Na sani a hukumar da ke kula da makarantu masu zaman kansu akwai sashe na musamman da ke kula da tabbatar da inganci, sai dai wannan sashe ba ya aikinsa domin ba ya bibiyar yadda muke gudanar da ayyuka a makarantunmu ballantana kuma ya shirya mana bita don karin gogewa da sanin makamar aiki. Sai dai mu kanmu mu shirya wa kanmu bita don samun horo a kan ayyukanmu,” inji ta.
Shugabar Kungiyar ta yi korafi game da yadda ake samun yawaitar bude makarantu masu zaman kansu a fadin jihar wanda ta dora laifin a kan gwamnati, “Yanzu ku dubi yadda ake bude makarantu masu zaman kansu a dan tsukin unguwa sai ka samu makarantu sama da hudu ko biyar, makarantun kuma idan ka hada su ba su yi guda daya ba, domin yawancinsu gida ne da bai wuce dakuna biyar ba ko garejin mota sai a mayar da shi makaranta. Ina ganin da gwamnati tana sa ido a kai da ba a samu karuwar hakan ba,” inji ta.
Ta yi kira da gwamnati cewa ya kamata ta sauke hakkin ’ya’yan kungiyar da ke kanta don samun dorewar kyakkyawar alaka a tsakaninsu “Babu shakka akwai kyakkyawar alaka a tsakaninmu da gwamnati don haka nake kira ga gwamnati da ta sauke duk wasu hakkokinmu da ke kanta don dorewar waccan alaka da ke tsakaninmu,” inji Shugabar.