kungiyar masu motocin sufuri a Kurosriba sun zabi sabbin shugabanni

kungiyar masu motocin sufuri na kasa a Najeriya, NARTO, reshen Jihar Kurosriba ta gudanar da zaben sababbin shugabanninta.Tun da farko dai kafin a gudanar zaben, an zargi wasu ’ya’yan kungiyar da mayar da hannun agogo baya, inda suka nemi dankwafar da zaben tare da son haifar da rudani kafin daga bisani da yardar Allah da […]

kungiyar masu motocin sufuri a Kurosriba sun zabi sabbin shugabanni
kungiyar masu motocin sufuri a Kurosriba sun zabi sabbin shugabanni

kungiyar masu motocin sufuri na kasa a Najeriya, NARTO, reshen Jihar Kurosriba ta gudanar da zaben sababbin shugabanninta.
Tun da farko dai kafin a gudanar zaben, an zargi wasu ’ya’yan kungiyar da mayar da hannun agogo baya, inda suka nemi dankwafar da zaben tare da son haifar da rudani kafin daga bisani da yardar Allah da kuma shiga tsakani da shugaban shiyyar Kudu maso kudu da ya zama mai sa ido aka gudanar da zaben cikin nasara.
An zabi Alhaji Mudi Ibrahim shugaba, yayin da aka zabi Alhaji Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Bala Ogoja a matsayin mataimaki. Sauran wadanda aka zaba sun hada da Muhammad Abbas da aka fi sani da suna Muhammadu Badarawa, Mataimakin Sakataren Kudi, sai Ahmad Usman, Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar.  Mukamin Sakatare da na Ma’aji sun tafi bangaren masu kula da dakon kaya. An dai raba mukaman gwargwadon kowane yanki na kungiyar ta yadda abin ba zai kawo wata baraka ba.
Bayan da aka rantsar da shugabannin kungiyar, sabon shugaban, Alhaji Ibrahim ya yi wa Aminiya karin bayani na dabaru da kuma hanyoyin da zai bi na ciyar da kungiyar gaba. “Za a samar da ci gaba fiye da yadda aka samu a baya, musamman idan ’yan kungiya suka ci gaba da bayar da hadin kai da kuma kyakkyawar gudunmawa da suka saba bayarwa. Za mu kula da ka’idar tuki da kuma maleji na tuki da hukumar kiyaye hadura ta kasa ta ce kowane direba ya kiyaye, musamman motocinsu da suke bin hanyar Kudu zuwa Arewa da sauran sassan kasa.” Inji shi.
Shi kuwa Alhaji Muhammad Abdullahi, muhimmancin hadin kai da ci gaban kungiyar ya nuna wa membobinta da kuma fatar kowa ya yi aiki tukuru, domin samun nasara. Domin, kamar yadda ya ce, babu wani ci gaba da za a samu matukar kai bai hadu ba, don haka wajibi ne kowa ya bayar da gagarumar gudunmawa domin ci gabansu da na kungiya.
Muhammad Abbas, daya daga cikin wadanda suka samu mukami a kungiyar, godiya ya nuna da hadin kai da aka samu tare da kammala zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.