kungiyar Masu Sayar da Motoci ta samar wa ’ya’yanta filaye

Kimanin mutum 150 daga cikin mambobin kungiyar Masu Sayar da Motoci ta Jihar Kano (Kano Automobile Dealers Association) suka amfana daga kokarin da kungiyar ta yi na samar musu da filaye a kasuwar sayar da motoci da ake kokarin ginawa a Unguwar Dawanau da ke karamar Hukumar Dawakin Tofa da ke jihar.Shugaban Kwamitin Amintattu na […]

kungiyar Masu Sayar da Motoci ta samar wa ’ya’yanta filaye
kungiyar Masu Sayar da Motoci ta samar wa ’ya’yanta filaye

Kimanin mutum 150 daga cikin mambobin kungiyar Masu Sayar da Motoci ta Jihar Kano (Kano Automobile Dealers Association) suka amfana daga kokarin da kungiyar ta yi na samar musu da filaye a kasuwar sayar da motoci da ake kokarin ginawa a Unguwar Dawanau da ke karamar Hukumar Dawakin Tofa da ke jihar.
Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar Ambasada Mukhtar Gashash ne Shugaban ya ce tun lokacin gwamnatin da ta gabata ta nemi wadannan filaye don a samar da kasuwar sayar da motoci ta musamamn a jihar.
“Mun dade kungiyarmu tana fafutikar yadda za ta samar wa ’ya’yanta filaye domin tun a lokacin gwamnatin Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi mana alkawarin samar da kasuwa ta masu sayar da motoci zalla. Sai ga shi alhamdulillahi burinmu ya cika mun samu gwamnatin ta fitar mana da filaye a wannan wuri, inda dillalan mota 150 suka samu filaye a ciki, kuma tuni aka damka wa kowanensu shaidar mallakar filin a hannunsa,” inji shi.
Ambasada Gashash ya ce tuni kungiyar ta tuntubi wasu Turawa da za su gina kasuwar ta yadda za ta dace da zamani. “Kasancewar idan aka bar mutane su gina runfunan da kansu zai lashe musu jarinsu, ya sa muka hada kai da wasu Turawa da za su gina mana kasuwar. Za a gina wurin bisa tsari hawa uku ta yadda zai ba wa kowa damar zabar irin ginin da yake so daidai karfinsa. Mun yi yarjejeniya da Turawan a kan cewa kowane mai fili zai biya su kudinsu cikin shekara 10. Za a samar da komai na bukatun rayuwa a cikin kasuwar da suka hada da ofishin ’yan sanda da kotu da bankuna da wurin canjin kudi da masallaci da coci da wurin sayar da abinci da gidan mai da sauran abubuwan da mutum zai iya gudanar da rayuwarsa ba tare da ya fiita waje ba.  Za a fara wannan gini  ne da zarar gwamnati ta kammala fitar da tituna da magudanun ruwa a wurin,” inji shi.
Game da irin muhimmancin da kasuwar ke da shi ga masu motocin, shugaban ya ce idan aka samar da kasuwar za ta tsabtace jihar daga matsalar cinkoson da motocin ke kawowa.
“Na farko hakan zai tsabtace Jihar Kano daga cinkoson da motoci da ’yan kungiyarmu ke sayarwa yake kawowa. Kasancewar ba mu da wadatattun filayen ajiye motoci hakan ya jawo wasunmu suke ajiye motoci a bakin tituna, wanda yakan zama takura ga masu amfani da hanya. Haka kuma kasuwar za ta samar mana da kwanciyar hankali kasancewar kashi 95 na ’ya’yan kungiyar hayar wurin da suke ajiye motocinsu suke yi wanda a duk shekara ake kara kudin hayar. Lamarin da yake ci wa duk wani mai sayar da mota tuwo a kwarya,” inji shi.
Daga nan ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su  dauki sabuwar kasuwar a matsayin ci gaba ga harkar kasuwancinsu.
“Gaskiya da amana su ne ginshikin bunkasar kowace irin harka da mutum ya sa a gaba. Duk wanda ya kafa kasuwancinsa bisa gaskiya da amana, to ko’ina ya koma abokan cinikinsa za su bi shi. Wannan abu da ya zo mana ci gaba ne a harkar kasuwancinmu, domin an tara mu a wuri guda cikin tsari. Idan mutum yana shiga kasashen da suka ci gaba a duniya zai tarar da cewa kusan kowane abu akwai kasuwarsa ta musamman. Zan yi amfani da wannan dama in yi kira ga sauran ’ya’yan kungiyarmu da ba su samu filin ba su yi hakuri insha Allah nan ba da dadewa za su kai ga samu, a yanzu haka muna tattaunawa da gwamnati don sake samar mana da wasu filayen,” inji shi.