Kungiyar Masu Shayi ta bukaci Buhari ya dubi tashin farashin kayan masarufi

Kungiyar Masu Shayi ta Najeriya ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya dubi matsalar tashin farashin kayayyakin shayi da sauran kayan masarufi da ake fama da shi a kasar nan.  Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Sha’aibu Abubakar ne ya bayyana bukatar kungiyar,  lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos. Ya ce, al’ummar Najeriya […]

Kungiyar Masu Shayi ta bukaci Buhari ya dubi tashin farashin kayan masarufi

Alhaji Shu’aibu Abubakar Shugaban Kungiyar Masu Shayi ta Najeriya

Kungiyar Masu Shayi ta Najeriya ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya dubi matsalar tashin farashin kayayyakin shayi da sauran kayan masarufi da ake fama da shi a kasar nan.  Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Sha’aibu Abubakar ne ya bayyana bukatar kungiyar,  lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos.

Ya ce, al’ummar Najeriya musamman talakawa sun amince cewa  Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, don haka  suka  jajirce kan  sai da ya koma kan kujerar shugabancin kasar nan.

“Don haka muna  fata Shugaba Buhari zai dubi al’ummar kasar nan, musamman wajen gudanar da ayyukan raya kasa kamar bunkasa bangaren ilimi da kiwon lafiya da hanyoyin mota da kuma duba matsalar tashin farashin kayayyakin masarufi,  domin a samu a rage radadin talaucin da ake fama da shi a kasar nan,” inji shi.

Kuma ya yi kira ga Shugaban Kasar ya tallafa wa wannan kungiyarsu da sauran kungiyoyin da suke gudanar da sana’o’i a kasar nan.

Ya ce,  a zangon farko na gwamnatin Buhari sun yi ta kai koke-kokensu zuwa Abuja, amma ba su samu nasarar share musu hawaye ba. Don haka ya yi fatan a wannan karo, za a tausaya musu a share masu hawaye musamman wajen magance musu matsalar tashin farashin kayayyakin da suke gudanar da wannan sana’a da su.

Daga nan ya yaba wa al’ummar Najeriya kan yadda aka gudanar da zaben Shugaban Kasa da  majalisun dokoki da na gwamnonin jihohi  lafiya.

Ya ce, babu shakka wannan babban abin farin ciki ne ga dukan al’ummar Najeriya kan yadda aka gudanar da wadannan zabubbuka  lafiya. Ya ce, wannan ya nuna cewa dimokuradiyya ta fara zama da gindinta a Najeriya.