kungiyar Masu Unguwanni sun koya wa matasa 120 sana’o’i a Kaduna
kungiyar Masu Unguwannin da ke Kaduna ta koya wa matasa 120 sana’oi a garin Rigasa na karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna. Sakataren kungiyar Umar Na’ibi Muhammad ne ya sanar da haka a zantawansa da Aminiya. Ya ce, “an shirya shirin ne da nufin koya wa matasa masu zaman kashe wando sana’oi a garin […]
kungiyar Masu Unguwannin da ke Kaduna ta koya wa matasa 120 sana’oi a garin Rigasa na karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.
Sakataren kungiyar Umar Na’ibi Muhammad ne ya sanar da haka a zantawansa da Aminiya. Ya ce, “an shirya shirin ne da nufin koya wa matasa masu zaman kashe wando sana’oi a garin Rigasa domin su samu abin dogaro da kai.” Ya kara da cewa: “Muna koya masu dinki ne da yadda ake yin sabulu da yadda ake yin turare da kuma horo kan sarrafa kwamfuta da sauran sana’o’i da zai taimaka masu a rayuwarsu,” inji shi.
Sakataren ya ce yanzu haka akalla suna da matasa maza da mata 120. Hakazalika, akwai wasu matasan da suma muke shirin yayesu nan ba da jimawa ba. “Matasa sun bamu hadin kai matuka wajen halaltar wannan sashe haka suma mutanen unguwa sun taimaka da kuma masu unguwannin wanda dama kungiyar tasu ce. Domin su ke da alhakin turu mana matasan da za’a koyawa sana’oin,” inji shi.