Kungiyar mata lauyoyi ta tallafawa matan da aka ci wa zarafi a Yobe
An gudanar da rabon tallafin ne a Damaturu.
Kungiyar Mata Lauyoyi ta Kasa (FIDA), reshen Jihar Yobe ta tallafa wa wasu mata su 30 da aka ci wa zarafi da kyautar barguna a Jihar.
Rabon kayan tallafin ya gudana ne a Damaturu, babban birnin Jihar tare da tallafin Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).
- NATO na kokarin hana China fadada karfin nukiliyarta
- Masu garkuwa da dan shekara 3 na neman kudin fansa na N2m
Da take jawabi a wajen rabon kayan, shugabar kungiyar ta FIDA, Hajiya Altine Ibrahim, ta ce tallafin zai taimaka musu wajen rage radadin halin kuncin da suka shiga sakamakon cin zarafin da aka yi musu.
Hajiya Altine, ta yi kira ga gwamnati da masu taimakon al’umma da su shigo wajen ba da tasu gudunmawar wajen rage radadin da matan da aka ci wa zarafin suke ciki.
Ta kuma gode wa kungiyoyin AHI da UNFPA kan yadda suke ba da taimakon su wajen kare yancin mata da hana ci musu zarafi, inda suke jiran gwamnatin Jihar ta Yobe ta tura dokar zuwa majalisar.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Hauwa Mohammad, ta gode wa kungiyar ta FIDA saboda tagomashin.