Kungiyar Mata Masu Da’awa ta Jihar Nasarawa ta samu yabo daga limaman Makka

An yaba wa ’ya’yan Kungiyar Musulmi Mata Masu Da’awah ta Kasa reshen Jihar Nasarawa game da hali nagari da suka nuna kafin da bayan aikin Hajjin bana da aka kammala kwanan nan. Babbar Ko’odinetar Kungiyar ta Jihar Hajiya A’ishatu Ibrahim ce ta yi wannan yabo a zantawarta da wakilinmu dangane da harkokin kungiyar. Ta ce […]

Kungiyar Mata Masu Da’awa ta Jihar Nasarawa ta samu yabo daga limaman Makka

Hajiya A’ishatu Ibrahim

An yaba wa ’ya’yan Kungiyar Musulmi Mata Masu Da’awah ta Kasa reshen Jihar Nasarawa game da hali nagari da suka nuna kafin da bayan aikin Hajjin bana da aka kammala kwanan nan.

Babbar Ko’odinetar Kungiyar ta Jihar Hajiya A’ishatu Ibrahim ce ta yi wannan yabo a zantawarta da wakilinmu dangane da harkokin kungiyar. Ta ce ba shakka mambobin kungiyar da suka tafi aikin Hajjin bana sun cancanci yabo idan aka yi la’akari da halin dattako da kyawawan dabi’u da suka nuna a lokacin da suke Kasa Mai tsarkin wanda hakan ya sa Babban Limamin Makka da sauran limaman Kasa Mai tsarki suka karramasu.

Ta bayyana cewa “Ina amfani da damar nan wajen yaba wa mambobin kungiyarmu ta mata masu da’awa a nan jihar musamman wadanda suka yi aikin Hajjin bana dangane da wannan abin alfahari da suka yi mana inda ya kai ga wadannan manyan limaman Saudiyya suka karrama mu ta gayyatarmu tare da shirya mana babbar liyafa a Makka kuma suka ba mu wasu kyaututtuka da lambobin yabo da sauransu bayan sun gayyaci dukkan ’ya’yan kungiyarmu ta da’awa daga dukkan jihohin kasar nan da suka je aikin Hajjin bana inda muka fafata a wata gasar tukuici da karatun Alkur’ani da sauransu da limaman suka shirya mana wanda a karshe muka yi nasara.”

Daga nan sai ta gode wa limaman Makka dangane da karamcin inda ta bukaci ’ya’yan kungiyar a jihar da kasa baki daya su ci gaba da nuna kyawawan halaye a duk inda suka tsinci kansu.

Hajiya A’ishatu Ibrahim ta kuma bayyana nasarorin da kungiyar ta cimma da suka hada da tallafa wa dimbin mata  Musulmi da kananan yara da marayu da marasa galihu da sauransu ta fannin ilimi da saka su a makarantun addini da na boko da biyan kudin makarantansu da taimaka wa kimanin mutum 65 da kungiyar ta musuluntar da su da sasanta rigingimu a tsakanin ma’aurata da shiryawa tare da gudanar da lacca a-kai-a -kai don wayar wa al’umma  da matasa kai dangane da illar shan barasa da kwaya da sauran munanan dabi’u.

Ta ce kungiyar takan ziyarci asibitoci da gidajen yari musamman a lokutan bukukuwa inda take tallafa wa marasa lafiya da fursunoni da kayayyakin masarufi da tufafi da biyan kudin belinsu da sauransu.

Dangane da kalubale da kungiyar ke fuskanta a jihar, ta ce manyan kalubalen sun hada da rashin hanyoyin sadarwa da za su rika aika wa mambobinsu sakonni da rashin abubuwan hawa da rashin isassun kudi inda ta ce sau da yawa ’ya’yan kungiyar ne ke dauki nauyin tafiya wa’azi da kansu da sauransu.

Ta ce duk da cewa a wasu lokuta idan suka gabatar wa gwamnatin jihar bukatarsu takan tallafa musu gwargwado amma yanzu suna matukar bukatar taimakon gwamnatoci a dukkan matakai da sauran cibiyoyi da ke tallafa wa kungiyoyin addinin Musulunci irin nasu da masu hannu da shuni Musulmi don ba su damar bunkasa harkokin kungiyar don cimma kyawawan kudirorinta na yadawa tare da bunkasa addinin Musulunci a jihar da kasa baki daya.