kungiyar Mata Musulmi Masu Da’awah ta Nijeriya za ta ba mata jari

Shugabar kungiyar Mata Musulmi Masu Da’awah ta Nijeriya, reshen Jihar Neja, Malama Rabi danladi Makun, ta jaddada aniyar kungiyar na ci gaba da samar wa matan da mazansu suka rasu jarin yin sana’o’i,  a jerin matakan da suke dauka na rage yawan mutanen da suka rungumi barace-barace, musamman a shiyyar Arewacin kasar nan.Malama Rabi ta […]

kungiyar Mata Musulmi Masu Da’awah ta Nijeriya za ta ba mata jari

Shugabar kungiyar Mata Musulmi Masu Da’awah ta Nijeriya, reshen Jihar Neja, Malama Rabi danladi Makun, ta jaddada aniyar kungiyar na ci gaba da samar wa matan da mazansu suka rasu jarin yin sana’o’i,  a jerin matakan da suke dauka na rage yawan mutanen da suka rungumi barace-barace, musamman a shiyyar Arewacin kasar nan.
Malama Rabi ta bayyana haka ne yayin da kungiyar ta raba wa wasu irin wadannan matan, su 40, jari don gudanar da sana’o’in da za su samu rufin asiri cikinsu da kula da marayun da aka bar su da su.
Shugabar ta gode wa bayin Allah da ke cigaba da bayar da gudunmuwar abin da ya sawwaka domin taimaka wa irin wadannan mata da sauran marasa galihu a tsakanin al’umma, sannan ta yi kira ga wadanda suka ci moriyar shirin su yi amfani da shi don gudanar da sana’o’insu.
Sakatariyar kungiyar, Malama Aminah Abdul-Mumini ta shaida musu cewa ana shirye-shiryen biya wa ’ya’yansu kudin zango na biyu da na uku, kamar na zangon farko.Ta bukaci su dage wajen ganin ’ya’yansu sun samu ilimin addini da na zamani, kuma da kula da tarbiyya.
Malama Aminah ta nemi iyayen su  daina dora wa ’ya’yansu talla, lamarin da ke sa ake yawan samun bacewar yara da ma hallakarsu ta hanyoyi mabambanta. Ta bayar da misalin abin da ya faru kwanan nan a Unguwar Kaje inda aka dakile yunkurin da wani mutum ya yi na sace yara biyu, wadanda aka aike su sayen agwaluman Naira 20.
Malama Fatima Umar, wadda ke da marayu 7 da ke zuwa makaratun Islamiyya da boko, tana daya daga cikin matan da  aka samar wa rabin buhun waken soya domin sana’arta, ta yi na’am da yadda aka gaggauta samar musu kayan gudanar da sana’arsu.
Kayayyakin da aka rarraba sun hada da agusho da shinkafa da waken soya da masara, kuma an tsara matakan bin diddigin ko matan suna amfani da su bisa yarjejeniyar da aka shiga da su kafin a ba su.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna