kungiyar Mata Musulmi ta yi taron ranar Hijabi a Abuja
Gamayyar kungiyoyin mata Musulmi karkashin inuwar kungiyar Mata Musulmi ta kasa ta gudanar da taronta na shekara-shekara a kan muhimmancin sanya hijabi ga mata Musulmi.Taron wanda kungiyar ta shirya mai taken: “Ranar Hijabi ta Duniya ta shekarar 2016” a Abuja, a karshen makon da ya gabata, ya hada dayin tattaki zuwa hukumar kare ’yancin dan […]
Gamayyar kungiyoyin mata Musulmi karkashin inuwar kungiyar Mata Musulmi ta kasa ta gudanar da taronta na shekara-shekara a kan muhimmancin sanya hijabi ga mata Musulmi.
Taron wanda kungiyar ta shirya mai taken: “Ranar Hijabi ta Duniya ta shekarar 2016” a Abuja, a karshen makon da ya gabata, ya hada dayin tattaki zuwa hukumar kare ’yancin dan Adam ta kasa don mika kokensu kan kiraye-kirayen da wasu ke yi game da hana sanya shi.
Shugabar kungiyar Hajiya Maryam Uthman, ta bayyana cewa sun shirya taron ne don su wayar da kan jama’a kan muhimmancin sanya hijabi ga Musulmi.
Ta ce sanya hijabi Ibada ce da Allah madaukakin sarki ya umarci Musulmi mata su rika sanyawa.
Ta bayyana cewa shekarar da ta gabata wasu mutane sun rika sukan hijabin da mata Musulmi suke sanyawa musamman saboda irin yadda kungiyoyin ’yan ta’adda suke yin amfani da shi wajen kai hare-haren bam.
Ta kara da cewa saboda haka ne kungiyar ta shirya taro a wannan shekarar don sauya mummunar fahimtar da wasu suka yi wa hijabi.
“Wasu sun yi wa hijabi mumunar fahimta har ma suna kiraye-kirayen a hana sanya shi. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka shirya wannan taro don mu fadakar da su cewa sanya hijabi ibada ne kuma Allah ne Ya yi umarni da mu sanya,” inji ta.
Har ila yau, ta soki wadanda suke da’awar cewa nuna tsaraicin mata shi ne wayewa da kuma ’yancin ’ya mace.
Ta ce sanya hijabi shi ne wayewa ga ’ya mace domin shi ne zai sanya ta fito cikin jama’a cikin mutunci da kwarjini da kuma girmamawa.
“Idan zuciya ta gyaru aka samu manufa mai kyau tare da tufafi mai tsari kamar hijabi to sai ka ga an samu mace ta gari wacce kowa zai yaba da ita,” inji ta.
kungiyar ta yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su bayar da himma wajen gano kungiyoyin ’yan ta’adda da ke yin amfani da hijabi don kai hare-hare.
A lokacin da kungiyar ta yi tattaki zuwa hukumar kare ’yancin dan Adam ta kasa, Sakataren Hukumar Farfesa Bem Angwe wanda Daraktan Bayar da Kariya da Bincike na Hukumar, Mista A.A Yakubu ya wakilta ya bayar da tabbacin cewa hukumar za ta ba su kariya tare da kare ’yancinsu don cimma burin da suka sanya a gaba.