Kungiyar Matasan Arewa ta nemi shugabanni su samar wa matasa mafita
Majalisar Matasan Arewa (NYA) ta bukaci shugabanni da dukan masu ruwa-da-tsaki da ke Arewacin kasar nan su farka daga dogon barcin da suke yi har suka mance da matsalolin da suke addabar yankin da suka hada da matsalar tsaro da rashin aikin yi da kuma almajirai. Shugaban kungiyar ta kasa Kwamared Ibrahim Waiyya ne ya […]
Majalisar Matasan Arewa (NYA) ta bukaci shugabanni da dukan masu ruwa-da-tsaki da ke Arewacin kasar nan su farka daga dogon barcin da suke yi har suka mance da matsalolin da suke addabar yankin da suka hada da matsalar tsaro da rashin aikin yi da kuma almajirai.
Shugaban kungiyar ta kasa Kwamared Ibrahim Waiyya ne ya yi wannan kira lokacin da kungiyar take kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar reshen Jihar Kano.
Waiyya ya ce lokaci ya yi da za a mike tsaye domin tunkarar matsalolin don guje wa da-na-sani ganin cewa lokaci na neman kure wa yankin Arewa.
Waiyya ya ce kungiyar NYA ta yanke shawarar wucewa gaba wajen tunkarar wadannan matsaloli ciki har da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasan yankin ke yi. “kungiya tana nan tana tunanin yadda za a ce an samar da wani yanayi da matasa za su taka rawa a abubuwan da suka jibanci siyasa da mulki. Haka kuma akwai matsala ta rashin aikin yi wacce Majalisar Matasan Arewa ke kokarin ganin an kawar da ita ta hanyar lalubo hanyoyin da za a sama wa matasa aikin yi don a magance zaman banza a tsakaninsu. Kuma muna kokari wajen ganin an kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasan,” inji shi.
Shugabannin kungiyar da aka zaba su ne Mustapha Muktar, Shugaba da Barista Maryam Jibril, Mataimakiyar Shugaba sai Habibu Uwais, Sakatare da Abbas Yakasai, Mataimakin Sakatare. Sauran su ne Sulaiman Idris, Sakataren Kudi da Usman Ahmad, Mataimakin Sakataren Kudi sai Abubakar dangambo, Sakataren Watsa Labarai sai Sadiya Inuwa Musa, Ma’ajin kungiyar.