Kungiyar matasan Kwankwaso ta gudanar da taronta a Gombe
kungiyar wayar da kan Matasan Kwankwaso na shiyar Arewa maso Gabas da ke goyon bayan tsayawar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso takarar shugabancin Najeriya a 2019 idan Buhari ba zai sake tsayawa ba mai suna North East Kwankwaso Youth Awareness Forum ta gudanar da taron ta na shiyar a garin Gombe. Da yake zantawa da Aminiya […]
kungiyar wayar da kan Matasan Kwankwaso na shiyar Arewa maso Gabas da ke goyon bayan tsayawar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso takarar shugabancin Najeriya a 2019 idan Buhari ba zai sake tsayawa ba mai suna North East Kwankwaso Youth Awareness Forum ta gudanar da taron ta na shiyar a garin Gombe.
Da yake zantawa da Aminiya a Gombe jim kadan bayan kammala taron nasu Koodinatan kungiyar na Arewa Maso Gabas Alhaji Musa Muhammadu Isa Madawakin Rangwam, ya bayyana cewa sun zabi Kwankwanso ya fito takara ne saboda kokarin sa na ganin shi ne zai iya kwatanta gyaran Najeriya.
Alhaji Musa Muhammadu Isa, ya ce suna zaga jihohin shiyar Arewa maso Gabas ne suna ganawa da kungiyoyi don tallata dan takarar saboda ganin cancantar sa domin babu Sanata ko Gwamna da a kasar nan yake zaga Najeriya idan abu ya faru don jajantawa jama’ar kasa kamar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Madawakin na Rangwam, ya kuma ce idan Allah Ya kai mu shekarar 2019, Kwankwaso ya zama dan takara to shi ne wanda ya cancanta a zaba saboda shi ne wanda ya dauki nauyin ‘Ya’yan talakawa a Jihar Kano sama da dubu 3000 da aka tura su karatu a bangarori daban daban a kasashen duniya wadanda idan suka dawo ba Kano kadai ne za su amfana da su ba kasa ne baki daya.
Ya kuma ce bayan nan ya dauki jari ya bai wa masu kananan sana’oi don inganta sana’ar su, kuma kyauta ba don su biya shi daga baya ba kuma Sanata Rab’iu Kwankwaso shi ne yake yawo jihohin kudanci kasar nan yake biyan tarar wadanda aka tsare a gidajen yari ba tare da nuna bambancin siyasa ko kabilanci ba.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar Najeriya da cewa duk wani mai kuri’a da ya tabbata Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zaba a zaben 2019 muddin Buhari bai tsaya ba domin Kwankwaso ne kawai za ka zaba ba ka yi nadamar zaben ka ba.
Shi ma Adamu Isa Muhammad, Koodinatan kungiyar Matasan Fulani ta kasa Fulbe Youth Kwankwasiya Nationwide da suka karbi bakoncin kungiyar Wayar da kan Matasan Kwankwason ya ce sun ji sun gani idan dai a kan Kwankwaso ne.
Adamu Isa Muhammad, ya kuma kara da cewa a lokacin da ake kokarin hana Fulani Makiyaya kiwo a wasu sassan Najeriya shi ne ya tashi a gaban Majalisa ya nuna cewa hakan ba dai dai bane suma ‘yan Najeriya ne dole kuma a bar su su yi kiwo a ko ina wannan ma a cewar sa ya isa yasa su zabi Kwankwaso sai dai idan Buhari ne kawai ya sake tsayawa.