Kungiyar Matasan Madobi ta jinjina wa dan majalisa kan tallafa wa marayu
Kungiyar Matasan Karamar Hukumar Madobi da ke Jihar Kano mazauna Kaduna ta yaba wa dan majalisar yankin Madobi Alhaji Kabiru Yusuf saboda taimaka wa marayu da yake yi a yankin. Kungiyar ta ce ta gamsu da yadda dan majalisar ya kafa kwamitin ci gaba da taimaka wa marayu da marasa galihu tun kafin rantsar da […]
Kungiyar Matasan Karamar Hukumar Madobi da ke Jihar Kano mazauna Kaduna ta yaba wa dan majalisar yankin Madobi Alhaji Kabiru Yusuf saboda taimaka wa marayu da yake yi a yankin.
Kungiyar ta ce ta gamsu da yadda dan majalisar ya kafa kwamitin ci gaba da taimaka wa marayu da marasa galihu tun kafin rantsar da shi.
Mai magana da yawun Kungiyar Matasan Madobi mazauna Kaduna, Malam Jafaru Na-Sa’a-da-Sa’a Madobi ya shaida wa Aminiya cewa yabon ya zama dole saboda yadda dan majalisar yake taimaka wa talakawa da kuma marayu a yankin madobi
Malam Jafaru ya ce dan majalisar ya tallafa wa marayu da ’ya’yan marasa galihu a lokacin azumi inda ya raba musu kayan abinci da tufafi. “Yabon wannan bawan Allah dan majalisarmu, Kabiru Yusuf ya zama dole kasancewar ayyukan alherin da yake yi tun ba a zabe shi a kujerar ba. Wannan ya sa muke ganin kafa kwamitin taimaka wa marayu da kuma kokari da yake nunawa na aiki da zai yi mana ya sa muka ga ya dace mu yaba masa mu mutanen Madobi mazauna Kaduna, don karfafa masa gwiwa,” inji shi.
Sai ya yi kira ga Shugaban Karamar Hukumar Madobi, Alhaji Lawal Yahaya da ya daure ya yi koyi da dan majalisar wajen inganta rayuwar talakawan yankinsa.
Ya ce yankunan Madobi suna bukatar ayyukan ci gaba musamman hanyoyi da makarantu da asibitoci da suke matukar bukatar gyara.
“Matsalar ruwan sha dai Allah Ya yaye mana ita, abin da ya rage mana yanzu shi ne matsalar hanyoyi da makarantu da asibitoci da al’ummarmu suke bukata. Sai kuma batun taimaka wa matasa da aikin yi,” inji shi.
Ya bukaci shugabannin siyasa na yankin su rika waiwayar mutanen Madobi mazauna Kaduna domin muna da yara da suka gama makaranta suke kuma neman tallafi.
Jafaru ya yaba wa gwamnatin Abdullahi Ganduje bisa kokarin da ta yi na magance matsalar ruwan sha da al’ummar Madobi da kewaye suka yi fama da ita a shekarun baya.