Kungiyar Miyetti Allah ta rabu gida biyu a Jihar Oyo
Al’ummar Fulani a Jihar Oyo suna ci gaba da tayar da jijiyar wuya kan zaben shugabannin Kungiyar Miyetti Allah da aka yi mako biyu da suka wuce, inda wani bangare na kungiyar ya nuna rashin amincewa da zaben tare da barazanar zuwa kotu. Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, Sarakunan Fulani da dukkan […]
Al’ummar Fulani a Jihar Oyo suna ci gaba da tayar da jijiyar wuya kan zaben shugabannin Kungiyar Miyetti Allah da aka yi mako biyu da suka wuce, inda wani bangare na kungiyar ya nuna rashin amincewa da zaben tare da barazanar zuwa kotu.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, Sarakunan Fulani da dukkan masu ruwa-da-tsaki na kungiyar Miyetti Allah daga kananan hukumomi 33 ne suka halarci taron da aka gayyace su a garin Iseyin domin zabar sababbin shugabanni bayan karewar wa’adin shugabannin da suka bar gado.
Amma wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, ba a yi zaben ba, amma “Shugannin kungiyar na kananan hukumomi 33 na Jihar Oyo da dattawa da dukkan ’ya’yan kungiyar sun amince da umarnin uwar kungiya daga Abuja na zaben Alhaji Ibrahim Jiji, wanda ya shafe shekara 8 a matsayin Mataimakin tsohon Shugaban Kungiyar Alhaji Yakubu Bello.
Mun amince da matakin da aka dauka ne saboda cancantarsa a fannin kwarewa da jagoranci da fahimtar hanyoyin hulda da mahukunta da jama’ar jihar baki daya musamman a wannan lokaci da muke fafutikar kwato ’yanci a kan sabuwar dokar kiwo da Gwamnatin Jihar ta kakaba mana. Da kuma matsalolinmu da manoma da batun satar mutane da garkuwa da su da ake dora mana laifi,” inji majiyar.
Ta kara da cewa: “Amma abin mamaki bayan kwana biyu da nada sababbin shugabannin sai wadansu suka koma gefe suna amfani da ’yan jarida don nuna rashin amincewa wanda daukar irin wannan mataki a wannan lokaci bai dace ba.”
Daya daga cikin mutum hudu da suka nemi tsayawa takarar Shugaban Kungiyar Alhaji Ibrahim Saliu, ya shaida wa Aminiya cewa “Ba mu amince da dora Alhaji Ibrahim Jiji da Shugaban Kungiyar ta Kasa Alhaji Muhammadu Kiruwa ya yi ba, domin an kauce wa tsarin mulkin kungiyar. Shi ya sa muka dauki matakin zuwa kotu ko a koma a yi zaben da kowa zai zabi wanda yake so.”
Haka Ibrahim Saliu, ya ce “Fulanin da ke zaune a Jihar Oyo sun kasu gida uku da suka hada da Bororo da Fulani Hausawa da Fulani Yarbawa, amma maimakon a kyale kowane bangare ya nuna bajintarsa sai kawai a dora bangare daya a kan dukkan mukaman aka manta da mu Fulanin Yarbawa da aka haifi iyaye da kakanninmu a nan. Ai ka ga ba a yi adalci ba ko kadan. Shi ya sa muka dauki matakin zuwa kotu.” Duk kokarin jin ta bakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jihohin Yamma Alhaji Kabir Labar da Aminiya ta yi abin ya ci tura. Amma a ranar Lahadi da ta gabata an hango Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Saliu Kadiri da Shugaban Kungiyar mai barin gado Alhaji Yakubu Bello da sabon Shugaba Alhaji Ibrahim Jiji suna tattaunawa a wajen taron kaddamar da sababbin shugabannin Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar da aka yi a Ibadan. Sai dai dukkansu sun yi gum da baki a lokacin da Aminiya ta nemi jin halin da ake ciki dangane da wannan al’amari.
Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Saliu Kadiri, wanda dansa Ibrahim Saliu ya tsaya takarar Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Oyo na daga cikin bangaren Fulanin Yarbawa da suke hamayya da sauran bangarori biyu na Fulanin Bororo da Fulani Hausawa.
“Muddin ba a hanzarta daukar matakin shawo kan wannan matsala ba, to za mu kwana a ciki kuma dukkanmu za muyi nadama domin yanzu ne Gwamnatin Jihar Oyo, za ta juya mu yadda take so a kan batun dokar kiwo da muke kokarin ganin an yi mata gyara,” inji wani Bafulatani da aka sakaya sunansa.