Kungiyar Miyetti Allah za ta kafa Kwamitin Zaman Lafiya tsakanin manoma da makiyaya
Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah reshen Kudancin Kaduna ta bayyana niyyarta ta kafa wani kwamiti da zai kunshi manoma da makiyaya musamman a wannan lokacin da makiyaya za su fara nada dabbobinsu don yin kaura saboda cin kara domin kauce wa samun matsala a tsakaninsu da manoman yankin. Shugaban kungiyar na shiyyar Kudancin Kaduna […]
Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah reshen Kudancin Kaduna ta bayyana niyyarta ta kafa wani kwamiti da zai kunshi manoma da makiyaya musamman a wannan lokacin da makiyaya za su fara nada dabbobinsu don yin kaura saboda cin kara domin kauce wa samun matsala a tsakaninsu da manoman yankin.
Shugaban kungiyar na shiyyar Kudancin Kaduna Abdulhamid Musa Albarka ne ya bayyana haka a yayin taron da kungiyar ta gudanar a garin Kafanchan a tsakanin ardodi da shugabannin kungiyar na kananan hukumomi takwas na yankin don samar da mafita musamman ganin gabatowar bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Shugaban ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta Tarayya su tuna da al’ummar Fulanin yankin da suka yi asarar muhallinsu da dukiyoyinsu a lokacin rikicin bayan zaben Shugaban Kasa na shekarar 2011 da ake shirin sake rabawa karo na biyu.
“Yawancin mutanenmu ba su samu komai ba a irin kudaden da Gwamnatin Tarayya ta bayar a shekarar 2015. Mutanenmu da suka yi asarar dukiyoyi masu yawa ba su samu komai ba ’yan kadan din kuma da suka samu bai taka kara ya karya ba. Sai ka ga wanda aka kona masa shago ya samu kudi amma wanda aka kona masa dabbobi wadanda su ne jarinsa shi ma ba a ba shi komai ba. Don haka muke tuni a kungiyance ga gwamnatin jiha da ta tarayya su tuna da mu a wannan karo,” inji shi.
Da yake nasa jawabi, Sheikh Isa Baffa daga Jihar Filato, jinjina wa Shugaban Miyetti Allah Alhaji Muhammad Kiruwa, Ardon Zuru ya yi bisa kyakkyawan shugabancinsa, sannan ya yi kira ga Fulani makiyaya su hada kansu tare da nuna goyon baya don cin gajiyar wuraren kiwo na zamani da Gwamnatin Tarayya da na wasu jihohi ke shirin samarwa don amfanar makiyaya.