kungiyar ‘MURIC’ ta nemi a maida 1 ga Muharram ranar hutu a Najeriya

kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya wato ‘Muslim Rights Concern’ (MURIC) karkashin jagorancin Ishak Akintola ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mai da ranar daya ga watan Muharram a matsayin ranar hutu kamar yadda daya ga watan Janairu yake ranar hutu a Najeriya. Wannan bukata dai na kunshe ne cikin wata takarda da […]

kungiyar ‘MURIC’ ta nemi a maida 1 ga Muharram ranar hutu a Najeriya

kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya wato ‘Muslim Rights Concern’ (MURIC) karkashin jagorancin Ishak Akintola ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mai da ranar daya ga watan Muharram a matsayin ranar hutu kamar yadda daya ga watan Janairu yake ranar hutu a Najeriya.

Wannan bukata dai na kunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga ofishin shugaban kungiyar Akintola, wacce kuma wakilinmu ya samu kwafen ta, ya bayyana cewa aiwatar da hakan zai tabbatar wa miliyoyin musulman Najeriya cewa gwamnati na la’akari da su cikin al’amuranta.

Ya kuma ce kamata ya yi gwamanti ta tattauna da Hukumar koli ta Harkokin Addinin musulunci ta Najeriya ‘National Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA) dake karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III, domin tabbatar da ranar daya ga watan na Muharram ya zama ranar hutu a kasar nan.

Daga karshe shugaban kungiyar ya ce idan aka yi haka, kwanakin hutun da musulman Najeriya za su samu bisa ga kwanakin watan musulunci za su zama hudu, sannan na addinin kirista za su zama biyar kamar yadda su ke tsawon lokaci ba tare da al’ummar musulmi sun yi korafi akai ba.