Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa za ta yi taro a Gombe

Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa za ta gudanar da babban taronta na kasa, karo na 8 a garin Gombe a mako mai zuwa. Babban sakataren kungiyar ta kasa Kwamared Bashir Dauda  ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos. Ya ce duk shekara ’ya’yan kungiyar daga ko’ina a ciki da wajen […]

Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa za ta yi taro a Gombe

Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa za ta gudanar da babban taronta na kasa, karo na 8 a garin Gombe a mako mai zuwa. Babban sakataren kungiyar ta kasa Kwamared Bashir Dauda  ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos.

Ya ce duk shekara ’ya’yan kungiyar daga ko’ina a ciki da wajen Najeriya sukan hadu su tattauna kan ci gaban kungiyar da ci gaban al’umma baki daya a irin wannan taro.

Ya ce a taron da za a yi a Gombe, za a fara shi ne ranar Juma’ar makon gobe a kammala ranar Asabar.

Ya ce a wajen taron ana sa ran halartar Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung da Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu na III da Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwanbo da ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

“A ranar farko ta fara taron, ’yan kungiyar za su ziyarci gidajen marayu da asibitoci. A rana ta biyu kuma za a gabatar da makaloli da jawabai daga manyan baki da suka hada da Dokta Aminu Gamawa na Jami’ar Baze da ke Abuja da sauransu,” inji shi.