kungiyar Musulmi ta yi zanga-zangar adawa kan kudus
Hadaddiyar kungiyar Musulmi ta Jihar Oyo da hadin gwiwar Gidauniyar kudus Foundation sun gudanar da wata zanga-zangar lumana, domin nuna rashin amincewa da ayyana birnin kudus a matsayin fadar kasar Isra’ila da Shugaban Amurika Donal Trump ya yi a ranar 6 ga wannan wata. Tun da farko, an fara gudanar da gangamin ne a harabar […]
Hadaddiyar kungiyar Musulmi ta Jihar Oyo da hadin gwiwar Gidauniyar kudus Foundation sun gudanar da wata zanga-zangar lumana, domin nuna rashin amincewa da ayyana birnin kudus a matsayin fadar kasar Isra’ila da Shugaban Amurika Donal Trump ya yi a ranar 6 ga wannan wata.
Tun da farko, an fara gudanar da gangamin ne a harabar zauren taro na Mapo da ke birnin Ibadan, inda Shaihunan malaman Musulunci da manyan masana kamar Farfesa Abdul Hafeez Oladosu da Alhaji Isa Akindele da Dokta Dawud Alaga da Dakta Abideen Olaiya da Shaikh Tajudeen Al-Adabiy da Farfesa Ishak Lakin Akintola suka suka gabatar da kasidu masu nuna kyama da rashin amincewa da ayyana sunan kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila da Gwamnatin Amurika ta yi.
Shugaban kungiyar, Alhaji Ishak Kunle Sanni da shugaban Gidauniyar kudus, Barrister Abdul-Rasheed Atta ne suka fara gabatar da jawabai a gaban al’umma maza da mata da suka halarci taron a Ibadan.
Gaba dayan kasidun da aka gabatar a wajen gangamin sun nuna cewa al’ummar Musulmi ba za su taba amincewa da irin wannan tsokanar fada da kasar Amurka take yi wa Musulmin duniya ba. Sun nemi dukkan Musulmin duniya su fito su nuna kyama da rashin amincewa da wannan mataki na kasar Amurka. Sun ce yin haka ya zama wajibi, musamman saboda kasancewar masallacin Al-Aksa a matsayin na biyu a duniya yana cikin birnin na kudus ne, wanda masallaci ne na Musulmin duniya ba Falasdinawa kadai ba.
Sun ce akwai wasu kasashen duniya da suka ci gaba da suka fitowa fili suna yin tir da Allah wadan wannan mataki da kasar Amurka ta dauka, wanda zai iya haddasa rikici a duniya.
Daga bisani kuma al’ummar Musulmi maza da mata sun gudanar da zanga-zangar lumana, inda suka yi doguwar tafiya a kasa suna rike da rubutattun kwalaye da ke nuna kyama da rashin amincewa da wannan mataki. Jami’an tsaro dauke da bindigogi ne suka yi masu rakiya, domin tabbatar da zama lafiya da kwanciyar hankali yayin zanga-zangar.