Kungiyar Naka-Sai-Naka ta bayar da tallafi a Katsina

Kungiyar Bunkasa Ci Gaban Al’umma ta Naka-Sai-Naka Community Development da ke Unguwar Shararrar Pipe a garin Katsina ta bayar da tallafin tufafi ga wadansu mabukata. Shugaban Kungiyar, Malam Sani Namadi ya ce: “Na kirkiro wannan kungiya ce tun ranar 29 ga watan Okbotar 2014 tare da mutum 10 kacal. Amma yanzu muna da mutane sama […]

Kungiyar Naka-Sai-Naka ta bayar da tallafi a Katsina

Shugaban Makarantar Kiwon Lafiya ta Sahlan Malam Muhammad Shafi’u lokacin yake karbar karramawar da aka yi masa

Kungiyar Bunkasa Ci Gaban Al’umma ta Naka-Sai-Naka Community Development da ke Unguwar Shararrar Pipe a garin Katsina ta bayar da tallafin tufafi ga wadansu mabukata.

Shugaban Kungiyar, Malam Sani Namadi ya ce: “Na kirkiro wannan kungiya ce tun ranar 29 ga watan Okbotar 2014 tare da mutum 10 kacal. Amma yanzu muna da mutane sama da 50. Sannan babban dalilin kafa kungiyar shi ne, ni dai mutum ne da ya yi yawo bakin gwargwado a Kudancin kasar nan, don haka na ga irin yadda kungiyoyi suke aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma. Idan muka duba akwai jama’a da yawa masu bukatar taimako; amma ba su samu.”

Ya ci gaba da cewa, sun raba ayyukan kungiyar zuwa gida uku. Na farko samar da mutanen da za su tafiyar da kungiyar. Sai samar wa kungiyar duk wasu takardun halaccin gudanar da ayyukanta a ko’ina cikin jihar. Sa’annan da samar da ofishin kungiya na dindindin.

Ya ce, suna halartar tarurrukan wasu kungiyoyi tare da ziyarar manyan mutane ko masana don koyar da ’ya’yan kungiyar kan yadda za su tafiyar da aikinsu. “Baya ga wannan, mun yi kokarin kawo ofishin Sibil Difens a unguwar domin magance matsalar kauraye da ta so zama ruwan dare,” inji shi.

Malam Sani Namadi ya ce tufafin su ne suka tara a tsakaninsu – ciki har da kayan maza da mata kimanin 40 da aka kiyasta kudinsu a kan Naira dubu 200.

Shugaban ya ce, tun kafuwar kungiyar, Alhaji Aminu Danbaba ne ya tava taimaka mata da Naira dubu 30. Sai dai kamar sauran kungiyoyin Kungiyar Naka-Sai-Naka tana fama da matsalar rashin kudi ko tallafi daga masu hali duk da irin ayyukan da take gudanarwa. Sannan kungiyar na ci gaba da kokarin wayar da kan jama’a kan muhimmancin taimaka wa al’umma ta hanyar kungiya; wanda hakan ke matukar karanci a tsakanin al’umma.

Shi dai raba wadannan kaya ya zo ne domin nuna farin cikin kungiyar bisa ga wata lambar karramawa da ta samu daga wata kungiyar a kan lura da ayyukan da take gudanarwa a tsakanin al’umma.

Shi kuwa Uban Taro a lokacin bayar da kayayyakin jinkan, Alhaji Sani BK ya ce idan da za a rika samun irin wadannan kungiyoyi cikin al’umma musamman a unguwanni; to kuwa da an samu ci gaban da ba za a tava mantawa da shi ba.

Uban Taron ya jinjina wa wadannan matasa da suka yi wannan tunani har suka fito da wannan kungiya wadda za a ce gwamnati ta shigo ta karve hannu biyu domin tana rage mata ayyuka a tsakanin al’umma.

Wadanda suka amfana da tallafin tufafin daga kungiyar, sun nuna jin dadinsu tare da yin addu’ar Allah Ya saka da alheri ga duk mai hannu a wannan aiki.