kungiyar Naka-sai-naka ta samu nasarori a Jihar Legas
Shugaban kungiyar Naka-sai-naka da ke unguwar Agirik a yankin Ikorodu a jihar Legas, Malam Salisu A. Isa ya ce kungiyarsu ta bambanta da sauran kungiyoyi saboda nasarorin da ta samu masu yawa.Malam Isa wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata ya bayyana cewa jajircewar shugabanni da […]
Shugaban kungiyar Naka-sai-naka da ke unguwar Agirik a yankin Ikorodu a jihar Legas, Malam Salisu A. Isa ya ce kungiyarsu ta bambanta da sauran kungiyoyi saboda nasarorin da ta samu masu yawa.
Malam Isa wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata ya bayyana cewa jajircewar shugabanni da hadin kan ’yan kungiyar ne ya janyo suka samu nasara.
Ya ce ‘A da muna zaune kara zube sai muka ga bai dace ba, sai muka kafa kungiya muka sa mata suna Nak-sai-naka, inda muka tattara masu sana’ar acaba da sayar da kayan gwari da masu shayi da masu aikin leburanci a cikinta. Kuma tun lokacin da muka kafa kungiyar mun samu nasarori masu yawa wadanda ba za su kirgu ba’.
Ya ci gaba da cewa ‘Daga cikin nasarorin da muka samu sun hada da taimakon junanmu da hadin kai da rajista a asibiti don taimakon ’yan kungiya da ba su da lafiya. Ba mu da wata matsala da ta fi karfinmu a yanzu’.
Tsohon sakataren kungiyar Elbashir Adam ya bayyana cewa babbar nasarar da kungiyar ta samu ita ce ta hadin kai tsakanin membobin kungiyar.
Maji-dadin kungiyar Abubakar Tukur ya ce da’a da biyayya ga shugabanin kungiya suna daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu. Ya kara da cewa manyan ayyukan da suka saka a gaba sun hada da kara bunkasa asusun kungiyar ta yadda idan wata matsala ta taso za a iya maganinta nan take.
Shi kuwa sakataren kungiyar mai ci Abdullahi M Sani ya bayyana cewa babbar matsalar da take damunsu shi ne yadda kabilun yankin suke kiran bahaushe Malam ko Mola.