kungiyar nakasassu ta bukaci ’ya’yanta su fito don kada kuri’unsu

Shugaban kungiyar nakasassu na Jihar Yobe Malam Bunu Ali ya hori mambobin kungiyarsu su fito kwansu da kwarkwata don kada kuri’unsu a zabe mai zuwa, sannan ya bukaci su zabi shugabannin da ke da kyakkyawan kudirin da zai inganta rayuwarsu. Shugaban kungiyar nakasassun ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke […]

kungiyar nakasassu ta bukaci ’ya’yanta su fito don kada kuri’unsu
kungiyar nakasassu ta bukaci ’ya’yanta su fito don kada kuri’unsu

Shugaban kungiyar nakasassu na Jihar Yobe Malam Bunu Ali ya hori mambobin kungiyarsu su fito kwansu da kwarkwata don kada kuri’unsu a zabe mai zuwa, sannan ya bukaci su zabi shugabannin da ke da kyakkyawan kudirin da zai inganta rayuwarsu.

Shugaban kungiyar nakasassun ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke cibiyar kula da nakasassu da ke garin Damaturu a ranar Litinin.
“Lokaci ya yi da za mu farka don kada a ci gaba da barin mu a baya a yayin gudanar da zabuka, ba don komai ba kuwa sai don ta hanyar zaben shugabanni nagari za a tuna da mu duk lokacin da al’amuran ci gaba ya taso, amma matukar muka gaza fitowa don zabar mutane nagari, to kuwa dole ne a ci gaba da barin mu baya.”
Shugaban ya kara da cewa a kodayaushe mafi yawan shugabannin kan manta da muradun nakasassu a yayin da duk wasu harkokin tafiyar da ci gaban kasa suka taso, “a ganina hakan na faruwa ne saboda mun gaza zabar shugabanni na kwarai, tun da yake yawan nakasassun da ake da su a Jihar Yobe da ma Najeriya sun zarta adadin yawan al’ummar wasu kasashe.”
Ya bukaci nakasassu su fito su kada kuri’unsu kada su yi la’akari da abin da za a ba su kafin zabe da kuma yayin gudanar da zaben, domin kuwa “zabe ne wanda yake tamkar jihadi ne ya tinkaro mu, don sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne komai kan iya gudana.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu