kungiyar Nakasassu ta koka kan wakilanta a taron kasa

Shugabannin kungiyar Nakasassu ta kasa (JONAPWD) sun koka da abin da suka kira yunkurin aikawa da sunayen wakilan bogi domin su wakilci kungiyar a taron  hadin kan kasa da gwamnatin tarayya ke shirin yi. A cewar nakasassun, sun gano wai an musanya sunayen wakilansu  da suka tura zuwa ga kwamitin shirya taron saboda haka dole […]

kungiyar Nakasassu ta koka kan wakilanta a taron kasa
kungiyar Nakasassu ta koka kan wakilanta a taron kasa

Shugabannin kungiyar Nakasassu ta kasa (JONAPWD) sun koka da abin da suka kira yunkurin aikawa da sunayen wakilan bogi domin su wakilci kungiyar a taron  hadin kan kasa da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
A cewar nakasassun, sun gano wai an musanya sunayen wakilansu  da suka tura zuwa ga kwamitin shirya taron saboda haka dole ne su koka tun ba a cutar da su ba.
Wannan kokawa tasu na kunshe ne cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun tsohon shugaban kungiyar, danlami Bashara, wanda kuma ya raba wa maneman labarai a Jihar Kaduna.
“Kwamitin da aka kafa domin shirya wannan taron kasa sun bukaci duk wata kungiya da jihohi da su aika da sunayen wakilansu, hakan ya sanya muka aika da sunayen wakilanmu. Amma abin mamaki, sai muka samu labarin cewa wani dan kungiyarmu ya yi amfani da takarda mai kanun kungiyarmu, wacce ya je aka yi masa ta bogi, shi ma ya aika da wasu sunayen na daban zuwa ga sakataren gwamnatin tarayya, wanda shi ne shugaban kwamitin shirya taron.
“Baya ga haka, muna kuma sane da cewa a yanzu haka sunayen wadanda za su wakilci kungiyarmu biyu aka tura zuwa ga kwamitin shirya wannan taron na kasa kuma ma’aikatun lafiya da na kawo cigaba ne suka aika da wadannan sunaye,” inji shi.
Ya kuma ce kungiyarsu na ganin ya dace su sanar da jama’a abin da ake cikin saboda kauce wa duk wani shiri da zai hana su halartar wannan  taron kasar.
kungiyar sun kawo misali da lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wanda shi ma a zamanin mulkinsa an yi irin wannan taron hadin kan kasa wanda kuma an baiwa kungiyar tasu damar zabar wakilanta ne ba tare da wani shisshigi ba daga waje..
Ya ce a kan haka suna ganin babu adalci idan kwamitin shirya wannan taro suka yi amfani da wani suna a madadin wanda ainihin kungiyar ta aika masu.
Nakasassun sun kuma bukaci gwamnati da ta baiwa na kasa su samu damar fadin abubuwan da ke damunsu a kasar nan.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50