kungiyar NAPO ta zabi sabbin shugabanni a Kaduna

kungiyar Tsofaffin Ma’aikatan Gidan Yari da Kwastam da kuma Hukumar Shige da Fice wato National Association of Paramilitary Officers (NAPO) ta zabi sabbin shugabanni a Jihar  Kaduna. Zaben wanda  aka yi a ranar Talatar makon jiya shi ne karon farko da kungiyar ta yi irinsa, kuma  an yi shi ne a gaban wakilin shugaban kungiyar  […]

kungiyar NAPO ta zabi sabbin shugabanni a Kaduna
kungiyar NAPO ta zabi sabbin shugabanni a Kaduna

kungiyar Tsofaffin Ma’aikatan Gidan Yari da Kwastam da kuma Hukumar Shige da Fice wato National Association of Paramilitary Officers (NAPO) ta zabi sabbin shugabanni a Jihar  Kaduna.
Zaben wanda  aka yi a ranar Talatar makon jiya shi ne karon farko da kungiyar ta yi irinsa, kuma  an yi shi ne a gaban wakilin shugaban kungiyar  ta kasa da kuma shugaban ’yan Fansho na Jihar Kaduna.
An yi zaben ne a cikin makarantar koyar da aikin Tsaron Gidan Yari da ke unguwar Barnawa a Jihar Kaduna.
Wanda aka zaba sabon Shugaban kungiyar shi ne Elder Ben Agbagu wanda a jawabinsa ya shaida musu cewa zai tabbatar da yin adalci ga kowa da kowa.
Ya ce “sanin muhimmancin kungiya ne ya sa suka ga ya dace a kafa kungiyar domin karbo hakkokinsu daga wajen gwamnati da kuma taimakawa mambobinsu lokacin da bukatar hakan ta taso.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da Mataimakin Shugaba wato Shehu Muhammed Shehu da  Sakatare Adamu Hassan da Mataimakin Sakatare  Yakubu Bello, sai ma’ajiya Misis Alabi da Sakataren Kudi  Shehu Abdullahi sai Sakataren Shirye-Shirye  Mista Kato.
Har ila yau, akwai mai ba da shawara a kan dokoki Ibrahim Umar sai kuma Jami’in Hulda da Jama’a (PRO)  Muhammad Abdulsalam.
A jawabinsa, wakilin Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Abdullahi Garba Gulu ya ce akwai kimanin hakkinsu na tsawon watanni 42 da gwamnati take rike musu.
Daga nan ya yi kira ga gwamnati da ta rika nuna kulawa ga tsaffin ma’aikata da suka yiwa kasa hidima a tsawon rayuwarsu.