kungiyar NAPPS ta koka kan yawan haraji
Shugabar kungiyar Masu Makarantun Kudi reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, wacce ake kira a takaice (NAPPS), Samira Jibir, ta ce yawan kudin haraji da gwamnati ke karba a wurinsu shi yake ci musu tuwo a kwarya. Shugabar wacce ita ce shugabar makarantar Glisten International Academy da ke Abuja ta yi furucin ne yayin da take […]
Shugabar kungiyar Masu Makarantun Kudi reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, wacce ake kira a takaice (NAPPS), Samira Jibir, ta ce yawan kudin haraji da gwamnati ke karba a wurinsu shi yake ci musu tuwo a kwarya.
Shugabar wacce ita ce shugabar makarantar Glisten International Academy da ke Abuja ta yi furucin ne yayin da take tattaunawa da Aminiya a ofishinta da ke harabar makarantar.
Ta ce kungiyarsu ta cimma nasarori masu yawa, amma babban abin da ke damunsu shi ne haraji iri-iri da gwamnati ke karba daga wurinsu.
“Babban abin da yake damunmu mu masu makarantu masu zaman kansu shi ne yadda gwamnati ke karbar haraji iri-iri daga wurin mambobinmu. Hukumomi kamar hukumar haraji ta kasa da masu fansho da sauran hukumomi duk suna matsa mana da karbar haraji. Wannan matsala ta dame mu,”inji ta.
Ta kara da cewa:“Mafiyawanmu da bashin bankuna muka dogara kuma muna biyan kudin ruwa mai yawa. Da wanne za mu ji. Da bashin bankin za mu ji ko kuma da haraji,” inji ta.
Daga nan sai ta bayyana cewa wata matsala da take damun su shi ne na karancin filayen da za su gina makarantunsu.
Ta dage a kan cewa mafi yawan filayen duk a wajen gari suke cikin daji ba tare da hanyar mota ba.
Daga nan sai ta ce kungiyar ta cimma nasarori masu yawa kamar hada kan mambobinta da ba da horo ga malamai don samun kwarewa a koyarwa da kuma wayar da kansu a kan cutar Ebola.
A ganinta babbar matsalar da ke damun malamai ita ce ta rashin kimanta su da girmama su tare da karancin ba su horo don kwarewa a kan aikinsu.
Ta ce “kowa ya raina malamai wasu iyayen ma zagin mu suke yi a gaban ‘ya’yansu wai don suna biyanmu. Wasu kuwa da sun rasa aikin yi sai su shiga harkar koyarwa ba tare da samun kwarewa ba. Ya kamata a gyara duk wadannan matsaloli muddin ana so harkar ilimi ta inganta.”