Kungiyar NAPPS ta nemi gwamnati ta samar da na’urorin kimiyya a makarantu
An yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da ingantattun na’urori da kayayyakin gwaje-gwaje na kimiyya a xakunan karatun makarantu don amfanin xalibai. Shugabar qungiyar masu makarantun kansu ta qasa wacce ataqaice ake kira (NAPPS), Dokta Sally NkemAdukwu-Bolujoko ita ta yi kiran yayin da take tattaunawa ta musamman da Aminiya a Abuja. “Ya kamata gwamnati […]
An yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da ingantattun na’urori da kayayyakin gwaje-gwaje na kimiyya a xakunan karatun makarantu don amfanin xalibai.
Shugabar qungiyar masu makarantun kansu ta qasa wacce ataqaice ake kira (NAPPS), Dokta Sally NkemAdukwu-Bolujoko ita ta yi kiran yayin da take tattaunawa ta musamman da Aminiya a Abuja.
“Ya kamata gwamnati ta daina vata lokaci ta samar da na’urorin zamani tare da ingantattun kayayyakin gwaje-gwaje a xakunan karatun makarantun gwamnati”.
Ta bayyana cewa yin hakan shi zai taimaka wajen bunqasa kimiyya da fasaha a makarantun gwamnati baki xaya.
Ta dage a kan cewa babu yadda za a samar da ingantaccen ilimin kimiyya da fasaha sai an samar da xakunan kimiya tare da sanya musu kayayyakin gwaje-gwage masu inganci.
Ta bayyana cewa sai da kayan gwaje-gwaje ne xalibai za su iya qwarewa tare da warware matsalolin kimiyya da fasaha.
Ta ce kayan gwaje-gwajen da aka tava kawo wa makarantu a shekaru masu yawa da suka gabata matsalar bambancin yaren Jamus da na Najeriya ya janyo aka kasa yin amfani da su a qasar nan.
“Kayan da aka kawo suna xauke da harshen Jamus shi ya sa ‘yan Najeriya suka kasa amfani da su hakan ya haifar da koma-baya tare da kawo cikas a fannin kimiyya da fasaha a qasa baki xaya,” inji ta.
Da ta juya kan fannin kayan karatu kuwa, Dokta Sally wacce qwararriyar malama ce ta nuna damuwarta dangane da halin da makarantun gwamnati suka tsinci kansu ciki na qarancin kayan karatu.
Ta bayyana cewa qarancin kayan karatu a xaukacin makarantu wata matsala ce da take neman agajin gaggawa.
Daga nan sai ta ja hankalin gwamnati ta qara himma wajen inganta vangaren kimiyya a makarantunta don a cewarta ta haka ne za a samar da ilimi mai inganci a qasa.