kungiyar NIPFOIRAb na so a ba ta gonaki don sama wa matasa sana’a
kungiyar farfado da martabar sarakunan Arewa da inganta harkar noma da kiwo (Northern Initiatibe for Promotion of Ideal Renaissance -NIPFOIRAb) ta bayyana aniyarta na gangami domin farfado da martabar sarakunan Arewa, tare kuma da cusa sabbin dabarun noma da kiwo a zukatan matasan Arewa domin ganin sun dogara da kansu wajen samun abin yi.Shugaban kungiyar […]
kungiyar farfado da martabar sarakunan Arewa da inganta harkar noma da kiwo (Northern Initiatibe for Promotion of Ideal Renaissance -NIPFOIRAb) ta bayyana aniyarta na gangami domin farfado da martabar sarakunan Arewa, tare kuma da cusa sabbin dabarun noma da kiwo a zukatan matasan Arewa domin ganin sun dogara da kansu wajen samun abin yi.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bala Alaramma Gombe shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Bauchi, bayan zaman da kungiyar ta yi a Kaduna, inda ta tattauna kan yadda za a samar da abin yi ga matasan Najeriya tare kuma da cusa musu dabarun sanin martabar magabatansu.
Alhaji Bala Alaramma ya bayyana cewa kungiyar na cikin jihohi 19 na Arewa da aka kafa saboda a farfado da martabar sarakuna da kuma harkokin noma da kiwo domin tallafa wa matasa domin su dogara da kansu, musamman ganin yadda aka mayar da ’yan Arewa saniyar ware saboda man fetur, “Alhali akwai sama da tsirrai 80 da idan an shuka a Arewa za su taimaka wajen bunkasa arzikinmu”. Inji shi.
Ya ce sai an dawo da martabar sarakunan gargajiya a Arewa, don lamurra sun lalace sosai ana kashe-kashe bisa son zuciya saboda rashin jagoranci na kwarai, don haka suka himmatu wajen neman gwamnonin jihohin Arewa su ba su hekta 300 a kowace jiha, su kuma za su nemo kudi daga gwamnatin tarayya da mawadata da za su kafa gonaki irin na zamani domin noma da kiwo a karkashin manyan sarakunan kowace jiha.
Haka kuma za su nemo kamfanonin da za su taimaka musu daga kasashen waje domin ganin an sama wa matasa a kalla dubu biyar aiki a kowace jiha ta Arewa.
Ya ce, da yardar Allah, idan suka samu goyon baya, za a kawo karshen wahalar da ake sha a Arewa, amma sai kowa ya sadaukar da kansa domin a tallafa wa yara wajen ganin tarbiyyarsu ba ta lalace ba, ta hanyar shiga miyagun ayyuka, wanda hakan ya sa suka himmatu suka zaga kan gwamnonin Arewa suka yi wa kungiyar rijista don ganin sun kama aikin tallafa wa Arewa gadan-gadan.
Alhaji Bala Alaramma ya bayyana cewa idan manyan Arewa ba su himmatu an gyara tarbiyyar matasa ba, akwai lokacin da za a zo mutum zai tara dukiyar mutane, amma ya gaza samun natsuwa. Ya ce kowane dan Arewa na da kishi, amma rashin masu tsayawa wajen ganin an yi abin da ya dace shi ya sa ake samun matsala, musamman wajen ganin yadda kaddara ke haifar wa Arewa matsalar rashin zaman lafiya da wargajewar zamantakewa da tattalin arziki.