kungiyar NLC ta jagoranci zanga-zanga a Owerri
Al’amuran al’umma sun tsaya cik a garin Owerri, babban birnin Jihar Imo, a ranar Larabar da ta gabata, a sakamakon wata babbar zanga-zangar ma’aikata da kungiyar kwadago (NLC) ta jagoranci gudanarwa saboda rashin biyan ma’aikatan jihar albashi.Shugabannin kungiyar kwadago na kasa da sauran kungiyoyin ma’aikatan kamfanoni daga Kudu maso gabas da Kudu maso kudancin kasar […]
Al’amuran al’umma sun tsaya cik a garin Owerri, babban birnin Jihar Imo, a ranar Larabar da ta gabata, a sakamakon wata babbar zanga-zangar ma’aikata da kungiyar kwadago (NLC) ta jagoranci gudanarwa saboda rashin biyan ma’aikatan jihar albashi.
Shugabannin kungiyar kwadago na kasa da sauran kungiyoyin ma’aikatan kamfanoni daga Kudu maso gabas da Kudu maso kudancin kasar nan ne suka yi gangami a Owerri, inda suka taya ’yan uwansu ma’aikatan jihar nuna kokensu, saboda rashin biyansu albashi.
Ma’aikatan, wadanda suka yi tattaki a tituna dauke da alluna rubuce da sakonnin nuna kin jinin gwamnati, sun dauki lokaci suna gudanar da zanga-zangarsu, wacce ta kasance ta lumana. Sai dai wannan tattaki da suka yi a tituna ya haddasa cinkoson ababen hawa da suka tsaya cik, ba-gaba-ba-baya, a garin Owerri.
A yayin da yake jagorancin masu zanga-zangar, Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Kwamared Ayuba Wabah, ya karfafa gwiwar ma’aikata a jihar cewa kungiyar tasu tana tare da su. Ya tausaya wa ma’aikatan, inda ya ce a Jihar Imo ne kadai ma’aikata ke bin bashin kudin albashi masu yawa ba tare da an biya su ba.
“A Jihar Imo a yau, ma’aikata da ’yan fansho suna bin hakkokinsu na albashi da alawus-alawus na tsawon watanni 15 zuwa 18. A wannan jihar ce kawai ake samun ma’aikatan shari’a suna bin bashin albashi na tsawon wata 8. Hatta malaman makaranta da suka yi ritaya, ba a biyan su fansho da sauran hakkoki. Kuma ina son a fahimta da cewa, babu wanda ke da ikon korar ma’aikata kawai a shafukan jarida, alhali an dauke su aiki ne bisa ka’ida kuma ta bin hanyoyin da suka dace, ba a jarida ba.” Inji Shugaba Wabah.
Ya ce sun kasance a jihar ce domin su kalubalanci Gwamna Rochas Okorocha ta hanyar tattaunawa da shi. Ya kara da cewa kungiyar NLC ba za ta launci duk wata makarkashiyar rage ma’aikata ko a rage masu albashi ba. Ya ce jam’iyyar APC a Jihar Imo ta yi hannun riga da kudurorin Shugaban kasa na kyautata wa al’umma. Ya ce maimakon ma a ce ana sama wa al’umma wasu ayyuka sabbi, shi gwamnan korar ma’aikata yake yi.
Shugaban na kwadago ya yi mamakin yadda al’amarin Jihar Imo ya tabarbare fiye da kima, duk da cewa ya samu tallafin kudin da Gwamnatin Tarayya ta ba shi a matsayin rance, don biyan ma’aikata hakkokinsu. Haka kuma ya yi Allah wadai da tsarin nan na gwamnatin jihar na sayar da kadarorin gwamnati da suka danganci asibitoci da wuraren kiwon lafiya a jihar. Ya ce wannan kamar rashin tausaya wa al’ummar jihar ne, ta hanyar danne masu hakkokin da suka wajaba a kan gwamnati.