kungiyar NUJ ta yi zaben cike gurbi a Katsina

kungiyar ’yan jarida (NUJ) ta kasa reshen Jihar Katsina ta yi zaben cike gurbi a ranar Asabar da ta wuce a sakatariyar kungiyar dake cikin babban birnin jiha. Shi dai wannan zabe na cike gurbin shugaban kungiyar na jiha,ya samo asali ne bayan sauka daga wannan mukami da shugaban kungiyar Abdullahi Izma Yamadi ya yi […]

kungiyar NUJ ta yi zaben cike gurbi a Katsina
kungiyar NUJ ta yi zaben cike gurbi a Katsina

kungiyar ’yan jarida (NUJ) ta kasa reshen Jihar Katsina ta yi zaben cike gurbi a ranar Asabar da ta wuce a sakatariyar kungiyar dake cikin babban birnin jiha.
Shi dai wannan zabe na cike gurbin shugaban kungiyar na jiha,ya samo asali ne bayan sauka daga wannan mukami da shugaban kungiyar Abdullahi Izma Yamadi ya yi jim kadan bayan gudanar da zaben Gwamnoni da aka yi a  watan Afirilun da ya gabata.
Kamar yadda dokar kungiyar ta tanada, za a cike gurbin duk wani mukamin da aka samu a cikin watanni uku bayan samun wancan gurbi. Sai dai an dan samu tsaikon yin wannan zabe a cikin lokaci saboda wasu ‘yan dalilai na yau da kullum da kungiyar ta samu kanta a ciki.
Kamar yadda shugaban kwamitin shiryawa tare da gudanar da wannan zade wanda kuma shi ne shugaban kungiyar wakillan sauran kafofin yada labarai dake cikin jihar (Correspondents Chapel) Alhaji Abdullahi ya shaida bayan kammala wannan zaben wanda ya samu kulawar Ferfesa Muhammad Yakubu, an samu ‘yan takara biyu da suka nemi wannan kujera. Abdullahi Aliyu ‘Yar’adua wanda ya fito daga gidan rediyon jihar ta Katsina wanda kuma shi ne babban Sakataren kungiyar na jiha, sai kuma Buhari Mamman Daura wanda ya fito daga ma’aikatar yada labarai ta jaha,wanda kuma a halin yanzu Darakta ne a ma’aikatar nan da ke yaki da yaduwar ciwon nan mai karya garkuwar jiki,wato SAKA dake jihar Katsina.
Wakillai 43 ne da suka fito daga kafofin yada labaran da ke jahar tare da na kungiyar wakillan suka jefa kuri’unsu don zaben wannan shugaba. Buhari Mamman Daura ya yi nasara da kuri’u 23 akan Abdullahi da ya samu kuri’u 20.
An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali tare kuma da karbar sakamakon zaben a yadda ya zo daga dukkan ‘yan takarar. Abinda aka kara neman haske akan wannan zabe shi ne,ta yadda shi daya dan takarar zai cigaba da zama bisa kujerarsa ta Sakatare wadda dama yana kanta ne ya yi takara. Cigaba da rike wannan mukami ya biyo bayan rashin samun wani bayani daga dokokin kungiyar akan irin wannan zabe, wanda dokokin ba su ce komai ba akan sauka ko rike mukamin da wani dan takara yake akai a lokacin da zai yi wata takara irin wannan a matakin jiha ko na kasa. A matakin rassa ne kawia aka yi bayanin saukar mai rike da wani mukami in yana so ya yi takara.
Da yake jawabi bayan rantsar da shi, sabon shugaban kungiyar Buhari Mamman Daura ya yi alkawarin rike wannan mukami bisa adalci ba tare da nuna bambanci ba, kuma ya yi alkawarin nemo hakkin ’yan kungiya a duk inda ya makale.
Buhari Mamman ya ce, zai yi kokari ya ga an yi amfani da kudaden ‘yan kungiyar da ake cirewa a duk wata bisa hanyar da ta dace. Har’ila yau, ya yi kira ga abokin takararsa wanda kuma yake abokin aikinsa ne da su hada hannu wuri daya domin ciyar da kungiyar gaba. Sannan ya nemi hadin kan sauran membobin kungiyar dake fadin jihar baki daya da su ba shi goyon baya tare da mukarrabansa don ganin haka ta cimma ruwa.