kungiyar NURTW ta bukaci agajin gwamnati

Sabon Shugaban kungiyar Direbobin Sufuri ta kasa (NURTW) reshen karamar hukumar Damaturu a Jihar Yobe Bulama Alhaji Usman ya roki gwamnatin jihar da ta duba matsalolin da ke addabar kungiyar don kawo musu daukin gaggawa.Shugaban ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu game da irin matsalolin da ya ci karo da […]

kungiyar NURTW ta bukaci agajin gwamnati
kungiyar NURTW ta bukaci agajin gwamnati

Sabon Shugaban kungiyar Direbobin Sufuri ta kasa (NURTW) reshen karamar hukumar Damaturu a Jihar Yobe Bulama Alhaji Usman ya roki gwamnatin jihar da ta duba matsalolin da ke addabar kungiyar don kawo musu daukin gaggawa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu game da irin matsalolin da ya ci karo da su bayan   darewarsa kujerar jagorancin kungiyar da suka dabaibaye ta wadanda wajibi sai gwamnatin jihar ne kawai za ta iya magance musu su, a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa manya-manyan matsalolin da suka fi addabarsu da suke bukatar gwamnatin jihar ta kawo musu dauki sun hada da neman a bude musu babbar kofar fita daga tashar motar garin Damaturu  wacce aka rufe ta fiye da shekaru hudu.
A cewarsa hakan ya tilasa musu amfani da kofa daya tak. “Wajen shiga da fita daga tashar ga masu abubuwan hawa sakamakon rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram da jihar ta fuskanta a baya, wadda hakan kan haifar musu cunkuso yayin shiga da fita,” in ji shi.
Daga nan ya ce kungiyarsu na ba da muhimmiyar gudummawa wajen samar da kudin shiga ga gwamnati ta fuskoki da dama da suka hada da yankan takardun mota da lasisi ga direbobi da kuma biyan kudin shiga tasha. Ya ce “saboda haka nake rokon gwamnatin jihar da ta gyara mana wannan tasha don yin kafada da kafada da tashoshin motar da ke hedkwatocin jihohi takwarorinta.”