kungiyar NURTW ta yi zabe a Katsina
Fiye da mambobi 400 ne suka jefa kuri’a a zaben sabbin shugabannin kungiyar direbobin sufuri ta NURTW reshen kananan motoci masu tafiyar dogon zango da ke cikin babbar tashar mota da ke cikin garin Katsina. A sakon da ya bayar ga masu zaben da wadanda aka zaba a ranar Asabar din makon jiya, Shugaban kungiyar […]
Fiye da mambobi 400 ne suka jefa kuri’a a zaben sabbin shugabannin kungiyar direbobin sufuri ta NURTW reshen kananan motoci masu tafiyar dogon zango da ke cikin babbar tashar mota da ke cikin garin Katsina.
A sakon da ya bayar ga masu zaben da wadanda aka zaba a ranar Asabar din makon jiya, Shugaban kungiyar Direbobin na Jihar Alhaji Sajen Muhammad Haruna wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Musa Abubakar ‘Yandoma, ya ja hankalin masu taron da su zamo masu kiyaye doka ne tare da jan hankalin ‘yan takarar da magoya bayansu da su rungumi kaddara kuma su bai wa juna hadin kai domin ciyar da kungiyar gaba.
Hakazalika, shugaban yayi kira ga mambobin kungiyar da su ci gaba da yi wa shugabannin kasar nan addu’a tare da kasar baki daya.
Bayan rushe shugabancin masu rike da kungiyar kamar yadda tsarin mulkinsu ya tanada kafin sake wani zaben, an yi tsawon sa’o’i bakwai ana gudanar da shi.
Mukamai bakwai ne daga cikin 17 aka yi takara yayin da sauran 10 aka yi babu hamayya. A cikin wadanda aka yi takarar sun hada har da na kujerar shugaba da mataimakan shugaba su biyu da babban sakatare da kuma ma’aji sakataren kudi.
Sabon shugaban kungiyar Alhaji Jamilu bayan godiya ya yi alkawarin jagorancin kungiyar bisa gaskiya da rikon amana, ba tare da nuna bambanci ba. Har ila yau, ya nemi hadin kan ‘yan kungiyar. Sannan ya bukace su da su ci gaba da zama tsintsinya madaurinta daya.