Kungiyar OPEC ta ce Matatar Dangote za ta kawo daidaito a Kasuwar Duniya
Kungiyar Kasashe masu Arzikin Fetur ta Duniya (OPEC) ta ce Matatar Man Fetur ta Dangote za ta kawo babban sauyi a bangaren samar da wadataccen mai musamman a Kasuwar Afirka nan da shekarar 2020. Kungiyar wacce take duba yadda harkokin mai yake gudana a duniya a halin yanzu, ta ce Matatar Dangote wacce ita ce […]
Kungiyar Kasashe masu Arzikin Fetur ta Duniya (OPEC) ta ce Matatar Man Fetur ta Dangote za ta kawo babban sauyi a bangaren samar da wadataccen mai musamman a Kasuwar Afirka nan da shekarar 2020. Kungiyar wacce take duba yadda harkokin mai yake gudana a duniya a halin yanzu, ta ce Matatar Dangote wacce ita ce irinta ta farko a Najeriya tana da karfin tace gangar mai dubu 650 a kowace rana.
A bisa ga kididdigar da aka gudanar a shekarar 2019 ganga miliyan 80 da dubu 622, kasashen duniya ke samarwa, kuma kashi 68 manyan kasashe ke samarwa yayin da kasashen kungiyar ke samar da kashi 44 cikin 100 a tsakanin mabobin kungiyar 14.
Kungiyar ta ce duniya tana tsammanin samun kari a shekarar 2020 wanda zai fito daga Kasuwar Najeriya ta hanyar gyara tsofaffin matatun mai da kuma sabuwar Matatar Dangote wadda aikinta yake gudana a halin yanzu. Kungiyar ta ce da zarar an kammala aikin matatar za a rage shigo da mai a yankin Afirka ta Yamma. “Tunda Matatar tana Yammacin Afirka ne aikin ba zai wadatar da yankin Kudancin Afirka da Gabashinta ba, amma matatar wata dama ce ta rage shigowa da mai da kuma samar da man a yankin,’’ inji kungiyar.
A cewar kungiyar, a kasashen Afirka akwai kimanin matatun mai kimanin 50 wadanda ake aikin gina su a halin yanzu kuma idan suka fara aiki za su tace akalla ganga miliyan 5 a kowace rana a nahiyar.
Da yake tsokaci a kan matsayin kungiyar, Shugaban Sashin Ayyukan Ci gaba na Rukunin Kamfanonin Dangote Mista Debakumar Edwin, ya ce kungiyar ta yi hasashen da ya dace kuma ya ce kamfanin a shirye yake ya kammala aikin a kan lokacin da aka tsara.
Ya kara da cewa kamfanin zai samar da kashi 100 na bukatun cikin gida ta hanyar samar da iskar gas da fetur da kananzir da kuma man jirgin sama sannan ya fitar da ragowar zuwa kasashen ketare domin cika muradin Kungiyar OPEC. Ya ce samar da mai wadatacce zai fitar da Najeriya daga sahun kasashe masu shigo da mai cikin gidansu sannan za ta zamo wacce take fiddawa zuwa ketare.