kungiyar OPEC ta ki zaben Diezani a matsayin sakatariyarta
A wani abin da ake ganin wani koma-baya ne ga gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan a kasashen duniya, kungiar kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta ki zabar Ministan Man na Najeriya Misis Diezani Alison-Madueke a matsayin Babbar Sakatariyar kungiyar. Wata kafar labarai ta ce kwana daya da Shugaba Jonathan ya mika sunan Misis Diezani wadda […]
A wani abin da ake ganin wani koma-baya ne ga gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan a kasashen duniya, kungiar kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta ki zabar Ministan Man na Najeriya Misis Diezani Alison-Madueke a matsayin Babbar Sakatariyar kungiyar.
Wata kafar labarai ta ce kwana daya da Shugaba Jonathan ya mika sunan Misis Diezani wadda ke fuskantar tuhumar almundahana don hawa wannan kujerar, Ministar ta gaza samun makin din da zai kai ta ga hawa wannan kujera a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci kungiyar.
A zaman wakilan kungiyar da aka gudanar a shekaranjiya Laraba wakilan kungiyar OPEC sun yanke shawarar kara wa’adin Babban Sakataren kungiyar Abdullah al-Badri na kasar Iraki har zuwa Yunin badi. Ana sanya ran zai bar kujerar a watan Disamban bana.
Shawarar OPEC na kara wa’adin Abdullah al-Badri da shekara biyu ya zo ne a ba-zata kuma ana ganin hakan a matsayin cin fuska ga Shugaban Najeriya.
Makusanta sun ce Jonathan ya yi tattalin zabenta don hawa wannan kujera tun hawansa mulkin kasar nan, duk da yadda ake zarginta da aikata almundahana.
Misali a watan Yunin 2012 ne zargin almundahana ga Misis Diezani ya fara fitowa fili lokacin da jaridar Sahara Repoters ta intanet ta fitar da wani bincike da ya bankado yadda ta kama dakunan kwana biyu mabambanta a wasu otel biyu masu tsada a birnin New York. Wannan ya faru ne a lokacin Babban Taron Majalisar dinkin Duniya na shekarar 2012.
daya daga cikin dakunan, da ke hawa na 28 a otel din Pierre Hotel an biya Dala dubu uku kusan Naira miliyan biyar a kwana guda. Jaridar ta kuma gano wani mai suna Joe Mordi, da ke aiki da Ministar a ofishin NNPC da ke Landan ya kama mata wani daki a wani fitaccen otel mai suna Four Seasons Hotel da ke tsakiyar birnin New York, inda aka biyar Dala dubu biyar ,kimanin Naira miliyan takwas da dubu 250 a kowane dare.
Misis Alison-Madueke, dai yanzu haka tana fuskantar matsi daga bangaren majalisar wakilai bayan da aka zarge ta da kashe Naira biliyan 10 na talakawan Najeriya wajen shatar jiragen sama don ayyukan kashin kanta a lokacin da take rike da mukamin Minista.,,,