Kungiyar PENGASSAN ta yi watsi da sayar da kadarorin mai

Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Albarkatun Iskar Gas sun gargadi gwamnatin tarayya kan sayar da manyan kadarorin man fetur don samar da kudin ga kasafin kudin shekarar 2018. Da yake mayar da martani ga rahoton da Aminiya ta buga inda ta ruwaito babban jami’in gwamnati yana cewa gwamnati na shirin sayar da kadarorin man […]

Kungiyar PENGASSAN ta yi watsi da sayar da kadarorin mai
Kungiyar PENGASSAN ta yi watsi da sayar da kadarorin mai

Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Albarkatun Iskar Gas sun gargadi gwamnatin tarayya kan sayar da manyan kadarorin man fetur don samar da kudin ga kasafin kudin shekarar 2018.
Da yake mayar da martani ga rahoton da Aminiya ta buga inda ta ruwaito babban jami’in gwamnati yana cewa gwamnati na shirin sayar da kadarorin man fetur don ta samar da kudi ga kasafin kudin shekarar 2018, Mai Magana da Yawun kungiyar PENGASSAN, Kwamared Fortune Obi ya bayyana cewa tana adawa da matakin kuma sauran ’yan Najeriya na adawa da matakin tun lokacin da aka kawo shi a shekarar 2016.