Kungiyar Rainbow ta lashe Kofin Magajin Garin Jama’a

Kungiyar kwallon kafa ta Rainbow Academy da ke garin Kafanchan A Jihar Kaduna ta lallasa takwararta ta Salama da ci 4-3 a bugun finareti bayan sun tashi da ci 2-2 a gasar cin Kofin Zaman lafiya na Magajin Garin Jama’a, Alhaji Abubakar Sadik Muhammad Isa da aka buga a filin wasa na Kafanchan, hedkwatar Karamar […]

Kungiyar Rainbow ta lashe Kofin Magajin Garin Jama’a
Kungiyar Rainbow ta lashe Kofin Magajin Garin Jama’a

Kungiyar kwallon kafa ta Rainbow Academy da ke garin Kafanchan A Jihar Kaduna ta lallasa takwararta ta Salama da ci 4-3 a bugun finareti bayan sun tashi da ci 2-2 a gasar cin Kofin Zaman lafiya na Magajin Garin Jama’a, Alhaji Abubakar Sadik Muhammad Isa da aka buga a filin wasa na Kafanchan, hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a.

Wasan wanda kungiyoyin kwallon kafa 16 suka fafata, an shirya shi ne don kara dankon zumunci a tsakanin matasa da nufin bunkasa zaman lafiya a Masarautar Jama’a da kewayenta wanda dan Sarkin Jama’a kuma Magajin Garin Jamaa’a ya dauki nauyin shiryawa.

A lokacin da yake jawabi yayin mika kyauta ga kungiyar da ta yi nasara, Fasto Emmanuel Kure na cocin Throneroom da ke Kafanchan kuma mamallakin gidan rediyon Salama FM da ke Kafanchan da kuma kungiyar kwallon kafa ta Salama da ta zo ta biyu a gasar, ya jinjina wa hangen nesan Magajin Garin Jama’a inda ya bayyana shi da yaro mai hangen nesa wanda ya tattara dukkan siffofin shugabanci.

Fasto Kure, wanda saboda tsananin farin ciki ya yi alwashin shirya kwatankwacin irin wannan gasar da za ta game dukkan Kudancin Kaduna, ya yi kira ga matasa da kada su bari ’yan siyasa daga kowace jam’iyya ko wasu malaman addini masu tsattsauran ra’ayi daga kowane bangare su kai su su baro ta hanyar amfani da su kan abubuwan da ba su dace ba.

“Ina kira ga matasa su dauki darasi daga irin wannan wasa wanda ya tattaro matasa daga kabilu da addinai daban-daban suka hadu a cikin kowane kulob suka fafata ba tare da la’akari da addinin mutum ko kabilarsa ba,” inji shi.

Shi ma da yake jawabin, Magajin Garin Jama’a Alhaji Abubakar Sadik tuni ya yi ga matasa kan su yi amfani da wannan dama wajen nuna wa duniya irin zaman lafiyar da ake yi a yankin a tsakanin kabilu kuma mabiya addinai daban-daban tare da fatar samun zaman lafiya mai dorewa da kulla zumunci a tsakanin juna.

A jawabin Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad wanda Danmadamin Jama’a, Alhaji Aminu Isa Muhammad ya wakilta ya nuna jin dadinsa kan shirya wannan gasa, inda ya ce hakan ba zai yiwuwa ba idan babu zaman lafiya. Don haka ya kara nanata kiran hadin kai a tsakanin matasan yankin baki daya.

Shugabannin Kwamitin Shirya Gasar, Alhaji Baballiya Musa da Matawallen Jama’a Alhaji Yusuf Baba Ahmad sun nuna jin dadinsu kan yadda aka fara gasar kuma a ka kare lafiya.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Salama FC; Bictor Obi aka zaba kocin da ya fi kowanne. Dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar kuwa shi ne Andrew Yusuf daga Rainbow Academy. Emmanuel Idika daga kungiyar Golden Balley ne ya zamo mai tsaron bayan da ya fi kowanne. Elias Monday daga Rainbow ne ya zamo mai tsaron gidan da ya fi kowanne yayin da Deco daga Salama FC ya zamo gwarzon dan wasa a gasar gaba daya.